Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles, ta taya ƙasar Sifaniya murnar lashe Gasar cin Kofin Duniya na shekarar 2026.
Cikin wani sako da Super Eagles ta wallafa a shafin ta na X jim kaɗan bayan Sifaniya ta doke zakarun da ke riƙe da kofi, Argentina, da ci 1-0 a wasan ƙarshe na ranar Lahadi, ta yi alƙawarin dawowa gasar a shekarar 2030.
“Muna taya ƙasar Sifaniya murnan lashe Gasar Cin Kofin Duniya na 2026… Sai mun hadu a 2030.”
-
Mbappe ya zama ɗan wasa na farko da ya lashe Takalmin Zinare sau 2 a jere
-
Spaniya ta lashe Kofin Duniya na shekarar 2026
-
Mun kafa tarihin da ba za a taɓa gogewa ba – Lionel Messi
A na sa ran cewa wannan saƙon zai kawo ƙarshen rashin halartar Najeriya Gasar, bayan ta kasa samun tikitin shiga gasar karo na biyu a jere.
Najeriya ta rasa damar shiga gasar ne bayan ta sha kayi a hannun Jamhuriyyar Kongo a birnin Rabat na Moroko, inda Najeriya ta sha kayi da ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Wannan ya ƙara tsawaita rashin halartar ta na shekaru 8 bayan ta gaza halartar wasan a shekarar 2022 da ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci.
