Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin mutane 26 a hukumomi da kwamitoci 10 na gwamnatin tarayya.

Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, a matsayin shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara (Rural Electrification Agency), sannan ya naɗa Manjo Janar Junaid Bindawa a matsayin shugaban Hukumar Albashi da Alawus ta Ƙasa (National Salary and Wages Commission).

Haka kuma, an naɗa Olajumoke Okoya-Thomas a matsayin sakatariyar Hukumar Albashi da Alawus, tare da naɗin kwamishinoni da mambobi bakwai na hukumar.

A gefe guda, an mayar da Tosin Johnson Adeyanju daga Hukumar Asusun Tallafa wa Caca ta Ƙasa (National Lottery Trust Fund) domin ya zama sakataren Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga da Rabon Kuɗaɗen Tarayya (Revenue Mobilisation and Fiscal Commission).

Shugaba Tinubu ya kuma naɗa Dakta Abuh Mohammed a matsayin Darakta Janar na Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (National Population Commission), sai Dakta Akinola Odeyemi a matsayin Manajan Darakta na Kamfanin Kasuwancin Wutar Lantarki na Ƙasa (Nigerian Bulk Electricity Trading), Dakta Anthony Godwin a matsayin shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya (Atomic Energy Commission), da Julius Oloro a matsayin Babban Daraktan Cibiyar Ƙasa ta Injiniyoyin Aikin Noma (National Centre for Agricultural Mechanisation – NCAM).

Sannan kuma an naɗa Dakta Abdullahi Maikano Saidu a matsayin shugaban Hukumar Kula da Bin Dokokin Kasafin Kuɗi (Fiscal Responsibility Commission), yayin da Shuni Muhammad Dahiru ya zama Babban Sakataren Hukumar Yaƙi da Jahilci ta Ƙasa. Haka kuma, an naɗa Gisaor Vincent Iorja a matsayin Babban Daraktan Kuɗi na Hukumar Gidaje ta Tarayya (Federal Housing Authority).

Sanarwar ta bayyana cewa dukkan waɗannan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *