Nasaran da Sifaniya ta samu a wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2026 ba wai kawai ta ba su ɗaukaka a fannin wasanni ba, har ma da babbar la’ada ta kuɗi.
A matsayinsu na sabbin zakarun duniya, La Roja za su karɓi dala miliyan 50 daga FIFA a matsayin kyautar gasar, yayin da Argentina da ta zo ta biyu za ta karɓi dala miliyan 33.
Ingila, wadda ta gama a matsayi na uku ta samu dala miliyan 27, Faransa da ta zo ta huɗu dala miliyan 27, yayin da ƙasashen da suka kai matakin kwata-fainal suka samu dala miliyan 19, yayin da ƙungiyoyin da suka kai zagaye na 16 suka samu dala miliyan 15.
-
Najeriya ta sauka zuwa mataki na 4 a Afirka – FIFA
-
Super Eagles ta sha alwashin shiga Gasar cin Kofin Duniya a shekarar 2030
-
Mun kafa tarihin da ba za a taɓa gogewa ba – Lionel Messi
Baya ga haka, kowacce ƙasa da ta buga gasar ta samu kuɗi na farko kusan dala miliyan 9 zuwa miliyan 10.5 samun gurbin halartar gasar, tare da ƙarin kuɗi domin ɗaukar wasu ɗawainiya.
Wannan ne mafi girman kyautar kuɗi da aka taba rabawa a tarihin Kofin Duniya, inda FIFA ta raba jimillar kuɗi dala miliyan 871 ga ƙasashe 48 da suka halarci gasar.
FIFA za ta tura kuɗaɗen ne zuwa ga Hukumomin Ƙwallar Ƙafa ta ƙasashe ba wai kai tsaye zuwa ga ‘yan wasanni ba
Idan aka hada jimillar kudi daga ko wane mataki, ana sa ran Sifaniya za ta samu fiye da dala miliyan 60 daga gasar, yayin da Argentina za ta samu Jimillar kuɗi kusa da dala miliyan 40–45.
