Ofishin Ministan Tsaro ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), na shirin yin murabus daga mukaminsa, inda ya bayyana lamarin a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da muguwar manufa
Mataimakiyar Ministan Tsaro kan Harkokin Yaɗa Labarai, Leah Katung-Babatunde, ce ta bayyana hakan a wata sanarwar da ta fitar
A cewar sanarwar, ofishin ministan ya samu labarin wasu rahotanni da aka yaɗa a kafafen intanet da ke cewa Janar Musa na shirin barin mukaminsa.
Sai dai ofishin ya ce wannan ikirari ba shi da wani tushe, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton
- Ana fargabar mutum 40 sun mutu bayan kwalekwale ya kife a Jigawa
- Dillalan mai sun ce shigo da fetur daga waje ya fi na cikin gida tsada
- Tsawa ta halaka yara, ta jikkata 2 a Adamawa
“Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) na ci gaba da mayar da hankali kan aikinsa na tsaron ƙasa, yana mai cikakken himma wajen sauke nauyin da aka ɗora masa da kuma jagorantar manufofin tsaron ƙasar, inda ake fara ganin sakamakon ƙoƙarinsa,” in ji sanarwar.
Ofishin ministan ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da masu amfani da shafukan sada zumunta da su guji yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba.
Ya ce ya kamata masu neman bayani su tuntubi ofishin ministan domin samun sahihin bayani kafin yaɗa wani rahoto.