Christos Tzolis, sabon dan wasan Arsenal

Arsenal ta sanar da kamala sayar dan wasan gefe, Christos Tzolis, daga Club Brugge, kan kwantiragin shekaru 5.

An gano cewa kudin da aka saye dan wasan ya kai fam miliyan 34, wanda shine mafi girma a tarihin gasar Belgium Pro League.

Dan shekara 24, wanda ya taɓa buga wa Norwich City, ya zura kwallaye 17 kuma ya bayar da taimako 23 a wasanni 36 na gasar a bara.

An sayo Tzolis ne domin ya maye gurbin Leandro Trossard, wanda ya tafi Besiktas kan fam miliyan 17. Duk da haka Arsenal na ci gaba da kokarin kawo wani babban dan wasan gaba, inda ta ke ci gaba da zawarcin Bradley Barcola bayan ta kasa samun Rogers.

“Abin ban mamaki ne na sanya hannu ga irin wannan babbar kungiya, zakaran Ingila,” in ji Tzolis.

“Zan yi alfahari da kasancewa cikin wannan tawaga a kaka mai zuwa.”

Darakta na wasanni na Arsenal, Andrea Berta, ya kara da cewa: “Christos dan wasan gaba ne mai iya buga wurare da dama. Ko da yake yana taka leda a bangaren hagu, yana jin dadin buga ko’ina a cikin fili.

Tzolis, wanda kuma dan wasan kasar Girka ne da kwallaye 9 a wasanni 34, zai sa riga mai lamba 17 a Arsenal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *