Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban Mulkin Soji, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya yi watsi da ikirarin da wani tsohon jami’in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Amachree, ya yi game da yadda marigayi shugaban ya rasu.
Al-Mustapha ya bayyana cewa bayanan da tsohon jami’in DSS ya wallafa a cikin littafinsa ba gaskiya ba ne, yana mai zargin cewa wasu ne suka rinjaye shi ya rubuta irin waɗannan bayanai.
- Sojoji sun fara aikin ceto Shugaban ƙaramar Hukumar Bunguɗu
- Gwamna Sule ya bai wa Nasarawa Amazons da sauran ƙungiyoyin wasanni kyautar kuɗi da mota
- Ku dawo gida don inganta fannin kiwon lafiya – Tinubu
“Wasu ne suka sa wannan yaron ya rubuta waɗannan ƙarerayin. Ina da dukkan bidiyoyin CCTV da suka ɗauki abin da ya faru, kuma abin da ya faɗa ba gaskiya ba ne,” in ji Al-Mustapha.
Ya jaddada cewa bayanan da ke cikin littafin ba su yi daidai da abin da ya faru ba, yana mai cewa yana da hujjojin da za su karyata ikirarin da aka yi game da mutuwar Janar Sani Abacha.
Al-Mustapha ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan iƙirarai, yana mai cewa bai dace a riƙa yaɗa bayanan da ba gaskiya ba ne a kan mutumin da ya rasu, wanda ba zai iya kare kansa ba.