Manyan jami’an Amurka na ganin cewa ƙarin hare-haren soji ba lallai ne su tilasta wa Iran komawa teburin sulhu ba.
Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan wata tattaunawa da Trump ya yi da manyan masu ba shi shawara da jami’an gwamnatinsa a ranar Juma’a.
Rahoton ya ce jami’an soji sun yi gargadin cewa sake faɗaɗa yaƙin na iya ƙara rage adadin makamai masu linzami na tsarin Patriot da sauran makaman kariyar sararin samaniya da ake amfani da su wajen kare dakarun Amurka da sansanoninta a Gabas ta Tsakiya.
- Super Falcons ta fitar da sabuwar rigarta mai taurari 10 kafin Gasar WAFCON ta 2026
- Gwamna Sule ya bai wa Nasarawa Amazons da sauran ƙungiyoyin wasanni kyautar kuɗi da mota
- Gwamnatin Tarayya ta baiwa tawagar ‘yan wasan ɗaga nauyi na masu buƙata ta musamman kyautar kuɗaɗe
Haka kuma, gwamnatin Trump na fargabar cewa ƙarin hare-hare kan Iran na iya jawo martani mai tsanani daga Tehran, da dagula dangantakar Amurka da ƙawayenta na ƙasashen Gulf, tare da ƙara ta’azzara matsalolin makamashi da na ’yan gudun hijira.
Rahoton ya ƙara da cewa Shugaban Majalisar Manyan Hafsoshin Sojin Amurka, Janar Dan Caine, ya yi gargaɗi a wani taro na sirri cewa sake shiga babban yaƙi da Iran zai iya rage yawan makamai masu linzamin kariya da hedikwatar tsaron Amurka ke da su a yankin.
Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar White House, Steven Cheung, ya ce Trump ya fi son a warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, amma ya ci gaba da riƙe dukkan damammaki idan Iran ta ci gaba da barazana ga Mashigar Hormuz ko ƙawayen Amurka.
Cheung ya kuma yi kira ga Iran da ta nemi cimma yarjejeniya, yana mai gargaɗin cewa idan ba ta yi hakan ba, za ta fuskanci sakamako.
A cewar rahoton, Trump na ci gaba da nazarin matakan da za a ɗauka kan rikicin da Iran, musamman yadda za a tabbatar da buɗe Mashigar Hormuz da kuma daƙile tashin farashin mai.