Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ƙaddamar da sabuwar jam’iyyarsa ta siyasa a ranar Asabar, domin ƙarfafa goyon bayan da yake da shi a tsakanin magoya bayansa.
Wannan mataki ya ƙara tabbatar da rabuwar kai a tsakanin Faye da tsohon amininsa amma yanzu abokin hamayyarsa, Ousmane Sonko, wanda ke jagorantar jam’iyyar da ke mulki ta Pastef.
Mutanen biyu sun yi fice, tare suka hau mulki a shekarar 2024 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar Pastef, kuma ana ganin za su iya fuskantar juna a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2029.
- MDD ta ayyana shekarun 2027 zuwa 2036 a matsayin shekarun ƙarfafa zaman lafiya a duniya
- Gwamnatin Jamus ta bayyana sharudan zama da ake buƙata kafin baƙi su nemi zama ‘yan ƙasar Jamus
- Trump ya dakatar da shirin ƙara tsananta matakan soji kan Iran
A makonnin da suka gabata kafin ƙaddamar da jam’iyyar Faye mai suna Kiray ko Republican Patriots, wasu jami’an jam’iyyar Pastef da dama sun yi murabus domin su koma bangaren shugaban ƙasar.
Wasu ‘yan adawa daga jam’iyyar Alliance for The Republic ma sun shiga sabuwar tafiyar Faye, ciki har da shugabannin yankuna da wasu mambobin ɓangaren matasa na jam’iyyar Pastef.
Haɗin gwiwar Faye da Sonko ya fara rushewa ne sakamakon sabani kan wasu muhimman manufofin gwamnati.
Daga cikin batutuwan da suka jawo rashin jituwa akwai yadda za a tunkari tattaunawa da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) kan shirin tallafin rance, a daidai lokacin da Senegal ke fama da matsalar yawan bashi.
Faye ya sauke Sonko daga mukamin Firayim Minista a farkon wannan shekarar, amma jam’iyyar Sonko ta ci gaba da riƙe da rinjayen kujeru a majalisa, sannan aka zaɓe shi a matsayin shugaban Majalisar Ƙasa jim kaɗan bayan haka.
An naɗa sabon Firayim Minista, Ahmadou Al Aminou Lo, a watan Mayu, amma an kafa majalisar ministoci ba tare da wani minista daga jam’iyyar Pastef ba, bayan Sonko ya bayyana cewa jam’iyyarsa ba za ta shiga cikin gwamnati ba
A shekarar 2024, Faye da Sonko sun yi kamfen tare bisa alkawuran samar da ayyukan yi ga matasa, yaƙi da cin hanci da rashawa, da kuma tabbatar da cewa Senegal ta samu kaso mai yawa daga kuɗaɗen da ake samu daga man fetur, iskar gas da ma’adinai.
Sai dai cika waɗannan alkawura ya ƙara zama mai wahala.
Ƙirƙirar sabuwar jam’iyyar Faye ta shirya fagen wata babbar fafatawar siyasa tsakanin tsoffin aminan biyu, wadda ake sa ran za ta bayyana sosai a zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2027, kuma tana iya yin tasiri ga kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na 2029.
