Ibrahima Yakubu

Yayin da duniya ke bikin Ranar Hana Mutuwa a Ruwa ta Duniya ta shekarar 2026, wanda ya karbi lambar yabo ta mako da lambar girmamawa ta hadin kan addinai ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Fasto Dr. Yohanna Buru, ya karrama uku daga cikin kwararrun masu ruwa na sa-kai a Jihar Kaduna saboda shekaru da dama da suka kwashe suna sadaukar da kai wajen ceto rayuka.

Lambar yabon ta zo ne domin nuna godiya ga gagarumin kokarin da suke yi wajen ceto wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a lokacin damina, da kuma hana yunkurin kashe kai da mutanen da ke fama da matsin rayuwa da tsadar abinci ke yi.

Yayin da ya kai ziyara Kogin Kaduna, Fasto Dr. Buru ya yaba wa masu ruwan na sa-kai saboda hidimar da suke yi wa bil’adama ba tare da tsoro ko rowa ba, musamman a lokacin damina lokacin da ambaliyar ruwa ke lakume rayuka da lalata dukiya.

A cewarsa, Ranar Hana Mutuwa a Ruwa ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 25 ga watan Yuli na kowace shekara, an kafa ta ne ta hanyar Kudurin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba A/RES/75/273, “Kariya Daga Mutuwa A Ruwa Ta Duniya,” wanda aka amince da shi a watan Afrilu na shekarar 2021.

Ya bayyana cewa wannan biki na duniya yana fito da mummunan tasirin da mutuwa a ruwa ke da shi a kan iyalai da al’ummomi, tare da inganta matakai masu amfani na kare aukuwar hakan.

Fasto Dr. Buru ya bayyana cewa kimanin mutane 236,000 ne ke mutuwa a ruwa a kowace shekara a fadin duniya, wanda hakan ya sa mutuwa a ruwa ta kasance daya daga cikin manyan dalilai goma da ke sanadin mutuwar yara ‘yan shekara 5 zuwa 14.

Ya kara da cewa sama da kashi 90 cikin dari na mace-macen da ke faruwa a ruwa suna faruwa ne a koguna, tabkuna, rijiyoyi, wuraren adana ruwa na gida, da wuraren ninkaya a kasashe masu karamin karfi da masu matsakaicin karfi, inda yara da matasa a karkara suka fi fuskantar wannan barazana.

Ya ce taken Ranar Hana Mutuwa a Ruwa ta Duniya ta shekarar 2026 ya mayar da hankali ne wajen inganta Tsarin Tsaron Duniya na Hana Mutuwa a Ruwa, wanda ake biki a ranar 25 ga Yuli na kowace shekara.

Fasto Dr. Buru ya yi kira ga kungiyoyin agaji da na jiyya da su tallafa wa masu ceton na sa-kai ta hanyar samar musu da kayayyakin ceto masu mahimmanci, musamman a lokacin ambaliyar ruwa.

Ya yaba wa masu ruwa na sa-kai na Kaduna saboda jajircewarsu wajen ceto wadanda ambaliya ta shafa da kuma mutanen da ke yunkurin kashe kansu a kogin kafin su mika su ga hukumomin da suka dace domin kula da su.

“Mun zo nan ne musamman domin mu karrama wadannan masu ruwa, sannan mu sanar da duniya cewa muna godiya da irin hidimar da suke yi da kuma sadaukar da kai wajen ceto rayuka a Jihar Kaduna,” in ji shi.

“Muna godiya ta gaske ga sadaukarwarku wajen ceto wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da kuma kare mutane masu rauni a cikin al’umma.”

Ya kuma bayyana cewa masu ruwan na sa-kai sun cancanci yabo na kasa saboda sadaukarwansu, musamman ga ayyukan ceto da suke yi a kewayen Kigo Road, Kabala, Tudun Wasa da ke kan hanyar Batsama, da sauran al’ummomin da ke kusa da Kogin Kaduna.

Da yake mayar da martani a madadin wadanda aka karrama, daya daga cikin amintattu kuma dattawan masu ruwa na sa-kai a Kaduna, Dattijon-Gada, ya nuna godiyarsa bisa wannan karramawa.

Ya gode wa Fasto Dr. Buru da tawagarsa bisa gane irin ayyukan jiyya da taimako da suke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *