Wasu masana kan harkokin shugabanci da tattalin arziki sun bukaci gwamnatin Najeriya ta soke Hukumar Tsara Jarabawar Larabci da Darussan Islama ta Kasa (NBAIS), suna masu cewa ayyukan da take yi na iya kasancewa karkashin wasu hukumomin jarrabawa da tuni suke aiki.

Da yake magana da jaridar Daily Trust, Daraktan Cibiyar CeFTPI mai sa ido kan kashe kudaden al’umma, Dakta Umar Yakubu, ya ce kasancewar NBAIS na daga cikin matsalolin tsarin shugabanci a Najeriya. Ya bayyana cewa an kafa hukumar ne duk da cewa akwai wasu hukumomi da za su iya gudanar da irin wannan aiki cikin inganci da gaskiya.

A cewarsa, bai kamata gwamnati ta ci gaba da kafa sabbin hukumomi masu maimaita ayyukan da wasu ke yi ba. Ya ce maimakon a kafa hukuma ta musamman domin gudanar da jarrabawa, ana iya bai wa hukumomi kamar WAEC da NECO, ko wasu cibiyoyin gudanar da jarrabawa, wannan nauyi.

Dakta Yakubu ya kara da cewa idan aka kafa hukuma mai maimaita aiki, hakan kan haifar da rashin inganci da kuma karancin ayyukan yi ga ma’aikatanta.

Ya yi zargin cewa hakan na iya bude kofar almundahana, yana mai cewa an dade ana zargin hukumar da daukar ma’aikata fiye da bukata.

Ya kuma yi ikirarin cewa mafi yawan ma’aikatan hukumar ba su da isasshen aikin yi, tare da cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta shafe shekaru tana gudanar da bincike kan wasu zarge-zargen da suka shafi hukumar, sai dai har yanzu ba a ji cikakken sakamakon binciken ba.

A cewarsa, mafi yawan kasafin kudin saye da sayarwa da hukumar ke warewa na iya zama wata hanya da ake samun cin hanci ta hanyar kwangiloli. Ya kuma yabawa JAMB kan yadda take gudanar da aikinta cikin inganci, yana mai cewa za a iya fadada aikinta domin kula da gudanar da jarrabawa gaba daya maimakon ci gaba da rike hukumomi masu irin wannan aiki.

Dakta Yakubu ya kammala da cewa yawan ma’aikatan da ke hukumar ya fi adadin mutanen da suke gudanar da jarrabawar da kanta, lamarin da ya bayyana a matsayin wata matsala a tsarin shugabanci da ke bukatar a sake duba ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *