Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayana dalilan da suka haifar da gaza gabatar da shugaban hukumar bogi Adeyemi Adeniyi gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai a ranar Laraba.

Cikin wata wasika da Sufetan ya aike wa kwamitin, wadda shugaban ta, Yusuf Gagdi ya karanta a ranar Laraba, ya bayyana cewa ba za’a iya kawo Adeniyi gaban kwamitin ba saboda ana tsare da shi ne bisa umarnin kotu.

Disu ya ce kaucewa umarnin ka iya jefa rundunar cikin hadari wanda ba’a fata. Amma idan ya zama dole to abune mai yiwuwa kotun ta nema ko kuma ta soke wannan umarnin ta.

Sai dai Shugaban kwamitin Honarabul Yusuf Gagdi ya ce kwamitin zai ci gaba da tattaunawa da rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa yayin da bincike ke ci gaba da gudana.

Kwamitin Majalisar Wakilan na bincike ne kan yadda ake zargin yadda hukumar ta bogi (PFIPC) ta samu gurbi a harabar Sakatariyar Gwamnatin Tarayya dake Abuja.

Da kuma samun kasafin kudi da ya zarce Naira Biliyan guda a cikin Dokar Kasafi ta Shekarar 2026, duk da ikirarin cewa ba a taba kafa hukumar ta hanyar doka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *