Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Turai, wato UEFA, ta yi barazanar ƙaurace wa duk wani gasar da FIFA za ta shirya idan Gianni Infantino ya ci gaba da shirinsa na siyar da wani kaso na hannun jari na Gasar cin Kofin Duniya.
UEFA ta ɗauki wannan matakin ne a taron gaggawa na dukkanin mambobin ta 55 wanda ya gudana a ranar Alhamis da yamma.
A cewar UEFA, “Mun yi fatali gaba ɗaya da shirin FIFA na sayar da hannun jarin Gasar cin Kofin Duniya da sauran gasar FIFA ga masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu.”
-
WAFCON 2026: Senegal za ta fafata da Kenya a wasa mai zafi
-
Neymar ya tabbatar da yin ritaya daga Brazil
-
WAFU B U20: Fying Eagles za ta kara da Sparrow Hawks
Wannan barazanar ƙauracewar ka iya rusa shirin Infantino gaba ɗaya, domin masu zuba jari ba za su yarda su zuba kuɗin su a gasar da ƙungiyoyin Turai ba za su halarta ba.
Gasar farko da UEFA za ta iya ƙauracewa ita ce Gasar cin Kofin Duniya na Mata ta 2027, wanda za a fara a ranar 24 ga watan Yuni na shekara mai zuwa.
FIFA ta sanar da cewa tana shirin ƙaddamar da wani shiri mai suna “FIFA Forward Enterprise – FFE”, wadda za ta siyar da hannun jari, ciki har da watsa shirye-shirye, ɗaukar nauyi, tikiti da lasisi da sauran su.
A ƙarƙashin wannan shiri, FIFA za ta tara har zuwa dala biliyan 4.2 daga wajen masu zuba jari ta hanyar siyar da ƙaramin kaso na FFE, wadda ta ce darajar ta na kusan dala biliyan 20.
Hukumar ta ce shirinta wanda ke buƙatar amincewar mambobin ta zai iya samar da sama da dala biliyan 10 na “kuɗin bunƙasa ƙwallon ƙafa” a cikin shekaru huɗu masu zuwa.
Sai dai UEFA, wato hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, ta fitar da sanarwa mai cike da fushi inda ta ce shirin ya “ketare iyaka”.
