Masu masaukin baki, Moroko, sun kara karfafa matsayinsu a rukunin ‘A’ na Gasar cin Kofin Kasashen Afirka ta Mata ta TotalEnergies CAF, bayan sun doke Algeria da ci 1-0 a wasa mai cike da tashin hankali a daren ranar Alhamis.

Sanaa Mssoudy ce ta zura kwallon da ta baiwa Moroko nasara a minti na 84, inda Atlas Lionesses suka samu nasarar karya tsaron gidan ‘yan Algeria.

Kasashen biyu sun shiga wannan wasa ne bayan sun samu nasara a wasansu na farko, inda Moroko ta doke Kenya 4-0 yayin da Algeria ta doke Senegal 2-0, lamarin da ya sa wannan wasa ya zama daya daga cikin mafi muhimmanci da tashin hankali.

Wannan sakamako ya sa Moroko ta samu maki 6 daga wasanni 2, kuma ta kasance cikin matsayi mai karfi na shiga wasan Kwata-fainal.

Ga Algeria kuwa, shan kashin ya musu zafi duk da bajintar da suka nuna na tsaron gidan su na tsawon lokaci akan masu masaukin bakin.

Algeria ta yi kokarin samun damar farke kwallan, amma Moroko ta tsaya da karfi har ta tabbatar da nasara ta biyu a jere.

Wannan nasara ta sanya Atlas Lionesses a saman rukuni na A da maki 6, kuma ta ci gaba da nuna kyakkyawan salon wasa a Gasar WAFCON da ake yi a gidan ta.

A wani labarin na daban, Senegal ta ci gaba da kiyaye burin ta na kai wa wasan Kwata-fainal na Gasar cin Kofin Kasashen Afirka ta Mata (WAFCON) ta 2026 bayan ta doke Kenya da ci 1-0 a Rabat, da ke kasar Moroko, ranar Alhamis.

Seynabou Mbengue ce ta zura kwallan da ta tabbatar da nasara a minti na 35. Da wannan nasarar ne Senegal ta samu maki 3 a gasar bayan ta sha kashi a wasansu na farko a rukuni na A a hannun Algeria.

Kenya ta yunkuro da karfin ta bayan dawowa daga hutun rabin farko, inda kyaftin din tawagar, Mwanalima Jereko da Tereza Engesha suka taka rawar gani, amma hakar su bai cimma ruwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *