Tambarin NFF

Kwamitin Zaɓe na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta NFF, ya fitar da tsarin gudanar da zaɓen Kwamitin Zartarwa na NFF na bana wanda aka tsara za a gudanar a ranar 27 ga Satumba a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.

Tsarin ya nuna cewa ranar Asabar, 1 ga Agusta za a fitar da dokoki da kuma kaidodin zaɓen, tare da fara sayar da fom, yayin da aka sanya ranar Laraba 12 ga Agusta a mtsayin ranar mayar da fom din da aka karɓa.

Sanar da ‘yan takara kan duk wata matsala da aka samu a cikin fom da aka miƙa wa Kwamitin zai kasance tsakanin 13 zuwa 19 ga Agusta.

Daidaita takardun ‘yan takara zai gudana tsakanin 20 zuwa 27 ga Agusta, yayin da tantance ‘yan takara zai gudana daga 27 zuwa 30 ga Agusta.

Za a fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da aka tantance a ranar 31 ga Agusta.

San nan kuma ‘yan takarar da aka kora za su samu damar miƙa ƙorafin su tsakanin 1 zuwa 3 ga Satumba, kuma za a kammala nazarin koke-koken na su daga 4 zuwa 10 ga Satumba.

Za a fitar da jerin sunayen ‘yan takara da aka tantance na ƙarshe a bainar jama’a tsakanin 11 zuwa 12 ga Satumba.

San nan kuma za a fitar da jerin wakilan da za su kaɗa kuri’a a ranar 13 ga Satumba.

‘Yan takarar da aka tantance za su iya fara yaƙin neman zaɓe daga 14 zuwa 24 ga Satumba, yayin da ranar 30 ga Satumba ita ce ranar ƙarshe ta mika koke-koke game da zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *