Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya farfaɗo daga matsanancin haɗarin durƙushewa gaba ɗaya, yana mai cewa an samu ci gaba a wasu muhimman alamomin tattalin arziki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Da yake magana kan yanayin tattalin arzikin ƙasar a wata hira da gidan talabijin na News Central Television, Sanusi ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji tattalin arziki mai fama da matsananciyar rashin daidaito sakamakon manufofin kuɗi marasa tsauri da kuma yawaitar fitar da kuɗi ba tare da kulawa ba a shekarun baya.

Ya ce matakan tsaurara manufofin kuɗi da aka ɗauka a cikin shekarar da ta gabata, ciki har da ƙoƙarin Babban Bankin Najeriya (CBN) na rage yawan kuɗin da ke yawo a kasuwa, sun taimaka wajen daidaita tattalin arzikin, duk da cewa hakan ya jawo wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa

Ya bayyana cewa darajar canjin kuɗi ta samu ɗan kwanciyar hankali, yayin da hauhawar farashi, duk da cewa har yanzu yana kusan kashi 20 cikin 100, ya fara raguwa daga matakan da aka samu a shekarun baya.

Tsohon gwamnan CBN ya kuma ce Najeriya ta ƙara ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen waje, inda ya bayyana cewa ajiyar ta haura dala biliyan 40.

Sanusi ya ƙara da cewa tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da sama da kashi uku cikin 100 a zangon farko na shekara, sannan ya haura kashi huɗu cikin 100 a zango na biyu, yana mai bayyana hakan a matsayin wani babban ci gaba.

Sai dai Sanusi ya jaddada cewa duk da alamomin ci gaban tattalin arzikin da aka samu, har yanzu hauhawar farashi da tsadar kuɗin ruwa suna ci gaba da zama manyan ƙalubale ga ‘yan kasuwa da gidaje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *