Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya Gianni Infantino, ya gudanar da wani taron gaggawa da manyan jami’an hukumar a ƙasar Morocco.

Yayin da ake ci gaba da samun kiraye-kirayen ya yi murabus bayan janye shirin buɗe gasar cin Kofin Duniya ga masu zuba jari masu zaman kansu.

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa taron ya gudana ne a ofishin yankin Afirka na FIFA da ke Sale, kusa da Rabat, domin tattauna rikicin da ya biyo bayan shirin da Infantino ya gabatar, wanda daga bisani aka soke saboda matsin lamba daga masu ruwa da tsaki.

Rahotanni sun nuna cewa Infantino na fuskantar suka masu tsanani, har ma daga cikin jami’an FIFA, kan yadda ya tafiyar da batun. Tun bayan da ya janye shirin a ranar Asabar da ta gabata, kiraye-kirayen da ke neman ya sauka daga mukaminsa sun ƙara ƙarfi.

An kuma ruwaito cewa Infantino ya nemi goyon bayan wasu tsoffin fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da ake kira “FIFA Legends”, amma hakan bai samu karɓuwa daga wasu ba.

Daga cikin waɗanda ake kyautata zaton sun halarci taron akwai Sakatare Janar na FIFA, Mattias Grafstrom, wanda wani saƙon imel da ya aika wa ma’aikatan hukumar yana sukar shirin ya bazu a kafafen yaɗa labarai ranar Talata.

Infantino,  ɗan ƙasar Switzerland mai shekaru 56, ya kasance a Morocco ne tun makon da ya gabata domin halartar bikin Ranar Hawan Karagar Mulki ta ƙasar.

Morocco na ɗaya daga cikin ƙasashen da za su karɓi bakuncin gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2030, kuma shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasar, Fouzi Lekjaa, na cikin kaɗan daga cikin shugabannin da suka fito fili suna goyon bayan Infantino bayan janye shirin.

Lekjaa ya bayyana cewa matakin da Infantino ya ɗauka na soke shirin ya kasance cikin hikima domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a cikin FIFA. Ya kuma sake jaddada goyon bayansa ga dukkan shirye-shiryen Infantino na bunƙasa ƙwallon ƙafa ta duniya a cikin shekaru goma da ya shafe yana jagorantar hukumar.

Kafin wannan rikici, Infantino ya kasance cikin farin ciki bayan nasarar gudanar da gasar cin Kofin Duniya mafi girma a tarihi, wadda ta haɗa ƙasashe 48 kuma aka shirya ta a haɗin gwiwar Canada, Mexico da Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *