Za a dawo buga Gasar Carabao Cup ta ƙasar Ingila ta kakar bana 2026/27, inda ƙungiyoyin da ke fafata Gasar Firimiya, Championship, League One da kuma League Two ke fafatawa tsakanin juna.
Za a fara wasannin zagaye na farko ranar Alhamis, yayin da Bristol City za ta karɓi baƙuncin Walsall a filin wasa na Ashton Gate.
Sannan kuma za a buga wasanni 3 a ranar Jumma’a da yamma, inda Wolves za su kece reni da Port Vale. Yayin da Middlesbrough za ta karɓi baƙuncin Wrexham. Sannan kuma daga ƙarshe, Stevenage za ta ziyarci Wycombe domin yin ta su karawar.
Gasar za ta ci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da za a shiga zagaye na biyu a cikin makon da zai fara ranar 24 ga Agusta.
Ƙungiyoyin Firimiyar Ingila guda 9 da ke buga Gasar Turai da suka haɗa da Arsenal, da Manchester City, da Manchester United, da Aston Villa, da Liverpool, da Bournemouth, da Brighton, da Sunderland da kuma Crystal Palace, za su shiga gasar ne a zagaye na uku.

Manchester City ce ta lashe kofin a bara bayan ta doke Arsenal da ci 2-0 a wasan ƙarshe.
Ƙungiyar Liverpool ce ta fi lashe Kofin Carabao a tarihi, inda ta ɗauka har sau 10. Ta fara lashe Gasar a 1981, sannan 1982, da 1983, da 1984, da 1995, da 2001, da 2003, da 2012, da 2022 da kuma 2024.
A cikin shekarun baya-bayan nan, Manchester City ta zama ƙungiyar da ta fi ko wacce ƙarfi a Gasar Carabao Cup.
Abin mamaki, Man City ta yi nasarar lashe kofin sau hudu a jere daga kakar 2017-18 zuwa 2020-21, wanda ya ƙara tabbatar da rinjayen ta a ƙwallon ƙafa ta Ingila a cikin shekaru goma da suka gabata.

Tun daga lokacin da aka fara wannan Gasa a kakar 1960-61, aƙalla ƙungiyoyi 23 daban-daban sun samu damar lashe kofin, wanda hakan ya ƙara wa gasar suna mai karfi a tsakanin magoya bayan ƙungiyoyin da ke shiga gasar.
Gasar tana ƙarƙashin kulawar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ingila, kuma tana baiwa dukkan kungiyoyi 92 daga manyan rukunoni 4 na Ingila damar fafatawa domin lashe wannan kofi mai daraja.
