Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya bayyana Hajiya Zeinab Ibrahim, Shugabar Matan APC na Arewa maso Gabas, a matsayin mataimakiyar sa a zaɓen gwamna na 2027.

Gwamna Kefas ya bayyana hakanne a ranar Jumma’a a Gidan TY Danjuma da ke Jalingo yayin ziyarar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Prof. Nentawe Yilwatda, wanda ya zo jihar domin bikin murnar cika shekaru 58.

Zeinab, ƙanwa ce ga marigayiya Sanata Jummai Al-Hassan, wadda aka fi sani da Maman Taraba.

Da yake jawabin maraba da baƙi yayin taron, Gwamna Kefas ya nuna Zeinab inda ya ce: “Ina maraba da ku zuwa wannan babban bikin taya murna na cika shekaru [58] na Shugaban Jam’iyyar mu na ƙasa – mataimakiyar gwamnan Jihar Taraba mai zuwa na zaɓen gwamna na 2027, Hajiya Zeinab Ibrahim. Na gode kuma barka da zuwa.”

Sanarwar ta jawo ihun murna daga mambobin jam’iyyar waɗanda suka dade suna jiran wannan mataki a hukumance.

Da yake tsokaci kan bikin cika shekarun, Gwamnan ya gode wa Frofessa Yilwatda bisa kawo tawagar likitoci zuwa Taraba a matsayin wani ɓangare na ayyukan murnar karin shekarun sa a duniya.

“Tawagar ku ta ‘Likitoci don bayar da magani da yin ayyukan tiyata Kyauta’ sun kasance a ƙasa suna aiki tsawon kwanaki. Mutanen Taraba sun shaida kuma mun yi matuƙar farin ciki,”* in ji Gwamna Kefas.

Ya ƙara da cewa Jihar Taraba za ta haɗa kai gaba ɗaya da Jam’iyyar APC domin mayar da kyakkyawan sakamako kan goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu ya baiwa jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *