Bisa la’akari da bayanan da kafofin yada labarai suka lakanto daga sabon Ministan Kudi Taiwo Oyedele (musamman lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa don amsa tambayoyi lokacin da aka nada shi Minista a Ma’aikatar Kudi), akwai wasu abubuwa biyar da zai baiwa muhimmanci.
Ko wanne daga cikin wadannan abubuwan kuma yana tattare da kalubale wanda ka iya yin kafar ungulu ga cimma biyan bukata.
Ranar Talata ne dai Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke Wale Edun daga mukamin Ministan Kudi, ya nada Taiwo Oyodele, wanda kafin nan Minista ne a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya.
- ‘Muna shirin mayar da Abuja cibiyar kudin bai-daya na Afirka’
- Minista ya roki masu kamfanonin jiragen sama da kada su daina aiki
- Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin bana
Ga manufofin da kalubalan:
1. Linzami ga hauhawar farashin kaya
Manufa: Daidaita darajar Naira da inganta hanyoyin samar da kayayyaki, da tabbatar da cewa kudaden mai suna shiga asusun gwamnati yadda ya kamata.
Ƙalubale: Sauyin farashin mai a kasuwannin duniya da matsalar wadatar da kasa da abinci na iya kawo cikas.

2. Sarrafa bashi a kan tsari
Manufa: Rage dogaro da rance, da tattaunawa don sake sharadin biyan bashin da kudin ruwansa ya yi yawa, da ƙarfafa amincin kuɗin Najeriya.
Ƙalubale: Matsin lamba na siyasa don ganin an samar da tallafi ko an samar da kudi don shirye-shiryen ba da tallafi ga jama’a ka iya kaiwa ga ƙara cin bashin.
3. Kwaskwarima ga tsarin haraji
Manufa: Haɗe nau’ukan haraji da nufin rage yawansu, da kare masu karamin karfi da ƙananan ’yan kasuwa, da tabbatar da daidaito a manufofin haraji.
Ƙalubale: Adawar masu muradu na kashin-kai da kuma matsalolin gudanarwa ka iya jinkirta aiwatarwa.
4. Tabbatar da gaskiya wurin tattara kudin shiga
Manufa: Toshe kpfofin tsiyayewar kuɗin shiga, da inganta shigowar kudade daga danyen man fetur, da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi ba tare da dogaro da mai ba.
Ƙalubale: Raunin hukumomin da za su aiwatar da yiwuwar almundahana ka iya tauye nasarar da za a yi.
5. Dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari
Manufa: Samar da tsayayyun manufofi masu kaifi daya don jawo masu zuba jari na cikin gida da na waje, da kuma ƙarfafa Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari.
Ƙalubale: Sauyin manufofin gwamnati ba zato ba tsammani ko tashin-tashinarsiyasa ka iya gurbata amincewar masu zuba jari.
