Gwamna Mai Mala Buni yace shima bai san wanda zai gaje shi ba.

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya mika wani babban sako na tunatarwa ga al’ummar jihar sa, inda ya jaddada cewa ikon bayar da shugabanci na Allah ne shi kadai, tare da yin kira ga mazauna jihar da su kauce wa rarrabuwar kai sakamakon siyasa.

Cikin wani sako da ya wallafa mai dauke da nazari kan makomar jihar sa, gwamnan ya bayyana cewa nasarorin da gwamnatinsa ta samu sun ginu ne a kan soyayya da amincin da jama’a suka nuna masa, sabo da haka yake ganin lokaci yayi da zai yi musu godiya.

“Ina so in gaya muku gaskiya wadda ta fito daga zuciyata, babu wanda ya san wanda zai zama gwamna nan gaba, ko ni kaina ban sani ba.”

Ya kara da cewa labarin rayuwar sa babban darasi ne, ya zama gwamna ne silar ikon Allah wanda ya wuce tsammaninsa. Saboda haka, ya bukaci ‘yan siyasa da magoya baya da su guji rarrabuwar kai, su kuma mayar da hankali kan ci gaban jihar a halin yanzu.

Matsayin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dattawan ke shawartar gwamnatin tarayya ta dakatar da al’amuran siyasa a wasu jihohin arewa, har sai tsaro ya inganta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *