Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeria (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa dangane da yanayin tattalin arzikin kasar nan, musamman yadda Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take ci gaba da karbo bashi, duk da cire tallafin man fetur.
A wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na News Central TV ya wallafa ranar Juma’a, Sanusi ya ce ko da yake yana goyon bayan matakin cire tallafin mai, akwai bukatar yin tambayoyi a kan inda kudaden da ake adanawa suke tafiya.
Ya kuma ce idan har an cire tallafin mai don Gwamnati ta samu rarar kudi, to bai kamata a ga ana ci gaba da loda wa kasar sababbin basussuka ba.
- Abubuwa 5 da Taiwo Oyedele zai baiwa muhimmanci
- ‘Muna shirin mayar da Abuja cibiyar kudin bai-daya na Afirka’
- Minista ya roki masu kamfanonin jiragen sama da kada su daina aiki
Sarkin ya jaddada cewa cire tallafin mai da kuma daidaita farashin musayar kudaden kasashen waje matakai ne da suka zama dole domin tserar da kasar nan daga durkushewa, lamarin da ya ce yadda aka dinga buga kudade a baya ne ya haddasa.
Ya yi karin bayani cewar shekaru takwas da suka gabata, Najeriya ta gudanar da rayuwar karya wajen karya farashin dala da bayar da tallafin mai, ta hanyar amfani da kudaden da ba a samar da su ba.
Sanusi ya kare matakan farko na Shugaba Tinubu a matsayin gyaran targade mai tsananin zafi da ya kamata a yi wa tattalin arziki, sai dai ya yi gargadin cewa rashin taka-tsantsan wajen kashe kudade da kuma yawan bashi ka iya lalata tasirin gyaran da ake kokarin yi.
Ya kuma nuna jin dadi da yadda Najeriya ta daina dogaro da shigo da man fetur daga ketare, yana mai cewa bunkasa matatun cikin gida kamar na Dangote babbar nasara ce ga tattalin arziki.
Sarkin dai ya shahara wajen bayyana ra’ayinsa kan manufofi da suka shafi tattalin arziki, kasancewarsa tsohon CBN a baya, sai dai wasu suna ganin kamata ya yi ya ja bakinsa ya yi shiru tun da a yanzu yana kan matsayi ne na sarauta, wanda ba kasafai ake son yawan magana ba.
