Shugaban Kasa Bola Ahmed TinubuShugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya zargi ;;yan adawa da q

Fadar Shugaban Kasa ta kare manufofin tattalin arzikin da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa, bayan sukar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi a kan yadda kasar nan take ciyo bashi.

Da yake mayar wa Sarkin martani a shafin X, daya daga cikin masu magana da yawun Shugaban Kasa, Daniel Bwala, ya ce matakan da Gwamnatin take dauka na ciyo bashi sun zama dole domin tunkarar matsalolin da aka gada daga gwamnatin baya.

Bwala ya jaddada cewa Gwamnati ba jin dadin karbar bashi take yi ba, tana kokari ne na toshe baraka da kuma samar da kudaden da za a gudanar da ayyukan raya kasa wadanda za su taba rayuwar talaka.

“Gwamnatin Tinubu tana gudanar da gyare-gyare ne a cikin yanayi mai wahala. Wadannan basussuka ana amfani da su ne ta hanyar da za ta kawo bunkasar tattalin arziki na dogon lokaci,” in ji Bwala.

Martanin na zuwa ne bayan da Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuwarsa a wajen wani taron kwararru, inda ya yi gargadin cewa Najeriya ka iya fadawa cikin matsin tattalin arziki idan aka ci gaba da karbar bashi ba tare da ingantattun hanyoyin biya ko kuma rage kashe kudin gwamnati ba.

Sarkin, wanda aka sani da kwarewa a fannin tattalin arziki, ya yi kira da a fito da wasu sababbin hanyoyi na samar da kudin shiga maimakon dogaro da bashi daga cibiyoyin kudi na duniya.

Wannan takaddama dai tana zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya suke ci gaba da fuskantar kalubalen tsadar rayuwa, lamarin da ya sa kalaman manyan mutane irin su Sarki Sanusi suke daukar hankali sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *