Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa kundin tsarin mulkin ƙasar na iya hana shi neman wa’adin mulki na uku, amma ya ƙi rufe batun gaba ɗaya .
Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da manema labarai a sansanin sojin Amurka na Joint Base Andrews.
Ya ce zai so ya sake tsayawa takara a zaben shugaban ƙasa na 2028, amma ya ƙara da cewa “Doka ta yi karfi sosai” wajen hana hakan.
Kalaman nasa sun zo ne bayan da wasu magoya bayansa suka riƙa kiran sunan “2028” a wani taro, lamarin da ya sake haifar da muhawara kan ko Trump na shirin neman ci gaba da mulki bayan wa’adinsa na yanzu.
Babban abin da ke hana Trump neman wa’adi na uku shi ne Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulkin Amurka ta 22.
Dokar ta ce ba za a iya zabar mutum a matsayin shugaban Amurka fiye da sau biyu ba.
Trump ya lashe zaben shugaban ƙasa a 2016, sannan ya sake lashe zaben 2024 bayan ya sha kaye a hannun Joe Biden a 2020.
Saboda haka, nasarorin Trump na 2016 da 2024 sun riga sun kai adadin wa’adin mulkin da kundin tsarin mulkin ya amince da shi, ko da yake wa’adin biyu ba su kasance a jere ba.
An kafa wannan dokar ne a shekarar 1951, bayan tsohon shugaban Amurka Franklin D. Roosevelt ya zama shugaban ƙasa na wa’adin huɗu .
Duk da wannan takunkumi na kundin tsarin mulki, Trump ya sha yin maganganun da suka nuna cewa yana ganin akwai yiwuwar neman wata hanya ta sake tsayawa takara.
A shekarar 2025, ya fadawa NBC News cewa ba wasa yake yi ba lokacin da yake magana kan yiwuwar wa’adi na uku.
- Zaben Gwamnan Osun, A Kididdige
- Najeriya ta rasa gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata
- Ba za a iya magance matsalar rashin tsaro a Najeriya da matakin soja kaɗai ba – Idris
Ya ce akwai “hanyoyi” da za su iya ba shi damar yin hakan, amma bai bayyana irin hanyoyin ba.
Wasu daga cikin magoya bayansa ma sun yi ta tattauna yiwuwar Trump ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa , sannan daga baya ya koma kan kujerar shugaban ƙasa ta hanyar tsarin maye gurbin shugaban, sai dai wannan ra’ayi na fuskantar babban kalubalen shari’a.
Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulkin Amurka ta 12 ta ce duk wanda bai cancanci zama shugaban ƙasa ba, bai cancanci zama mataimakin shugaban ƙasa. A ka’ida ana iya sauya ko soƙe Kwaskwarimar ta 22, amma hakan na da matuƙar wahala.
Dole ne a samu amincewar kashi biyu bisa uku na Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa, sannan jihohi 38 daga cikin 50 su amince da sauyin.Masana kundin tsarin mulkin Amurka sun ce irin wannan sauyin yana da matukar wahala, yayin da duk wata hanya ta kauce wa dokar za ta iya fuskantar kalubalen kotu.
Sabbin kalaman Trump sun nuna cewa ya fahimci cewa kundin tsarin mulkin Amurka na da babban shinge ga sake tsayawarsa takara.
A baya ma Trump ya taba cewa zai “so” ya sake tsayawa takara, kafin daga bisani ya amince cewa kundin tsarin mulkin Amurka bai ba shi damar yin hakan ba.
A halin yanzu, ba a bayyana ko ambaton shekarar 2028 da Trump ke yi dabarar siyasa ce ta faranta ran magoya bayansa, ko kuma wani yunkuri ne na gwada iyakokin kundin tsarin mulkin Amurka.