Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage sauraron karar da kungiyar Tsoffin ‘Yan Majalisa ta shigar tana neman a soke rijistar jam’iyyun ADC da Jam’iyyar Accord da ZLP da kuma AA.
Kungiyar tana zargin jam’iyyun adawar da saba wa Sashe na 225 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda ya bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) damar soke jam iyyun da suka gaza samun nasara a zabubbuka.
Da yake sanar da dage sauraron karar, Mai Shari’a Peter Lifu ya sanya ranar 5 ga watan Mayu domin ci gaba da zama, bayan amincewa da bukatar masu karar ta yi wa takardunsu garambawul, domin hadawa da sauran jam’iyyun siyasar da suke zargi da take dokokin Kundin Tsarin Mulki.
- Jam’iyyun adawa za su tsayar da dan takarar Shugaban Kasa guda
- Gaskiya a sadarwa tsakanin gwamnati da talakawa wajibi ce —Ministan Yada Labarai
- ADC ta karbe shugabancin marasa rinjaye a Majalisar Dattawa
Yayin da yake yanke hukuncin na wucin gadi, mai shari’a Lifu ya umarci dukkan bangarorin da ba su riga sun mayar da martani kan sababbin takardun karar ba da su gaggauta yin hakan.
Ya jaddada cewa lamarin yana da matukar muhimmanci ga muradan jama’a.
Alkalin ya nuna cewa duba da kusantowar zabubbukan fid da gwani na jam’iyyu gabanin babban zaben shekarar 2027, ya zama dole a kammala shari’ar cikin hanzari.
Ya bayar da umarnin cewa dukkan bangarori su shigar da hujjojinsu kafin ranar 1 ga watan Mayu.
Tsofaffin ‘yan majalisar suna neman kotu ta tilasta wa INEC hana wa jam’iyyun shiga duk wani taron siyasa ko zabe har sai sun cika ka’idojin doka.
Masu karar sun ce barin wadannan jam’iyyu su shiga zaben 2027 zai janyo asarar kudin gwamnati, sannan ya rage darajar tsarin zabe.
Sai dai jam’iyyar ADC ta kalubalanci wannan kara, tana mai cewa ba ta da tushe a shari’ance.
Ana sa ran ranar 5 ga Mayu za a fafata tsakanin lauyoyin kowane bangare a wannan shari’a mai matukar daukar hankali.