Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta sallami kocin tawagar Super Falcons, Justine Madugu, tare da dukkan mataimakan sa daga aikinsu nan take.
NFF ta sanar da hakanne a ranar Litinin a shafinta na X, bayan rashin nasarar tawagar Super Falcons a Gasar WAFCON ta 2026 da aka buga a Marokko.
“Kwamitin zartarwa na NFF ya yanke shawarar rusa tawagar masu horarw da Super Falcons,” in ji sanarwar.
-
Gusau ya ƙaddamar da kwamitin bincike na NFF
-
Galatasaray ta yi fatali da tayin Arsenal akan Victor Osimhen
-
Bruno Fernandes ba na sayarwa ba ne
Super Falcons ta gaza kaiwa wasan kusa da na ƙarshe na Gasar WAFCON, wanda hakan ya kawo ƙarshen begen samun tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027 da za a yi a Brazil.
An nada Justin Madugu a shekarar 2024 akan buƙatar tabbatar da samun tikitin zuwa Gasar Duniya. Amma hakan bai samu ba biyo bayan cire tawagar a matakin wasan kwata-fainal na Gasar WAFCON ta 2026.
NFF ta ce ta ɗauki wannan matakin ne don samar da sauyi a ɓangaren jagorancin tawagar da kuma mayar da ita matsayinta na wadda ta fi fice a nahiyar.
Da take martani kan wannan lamarin, kyaftin ɗin tawagar, Rasheedat Ajibade, ta buƙaci magoya baya su ci gaba da bayyana ƙwarin gwiwa yayin da tawagar ke shirin mayar da hankali kan wasanni masu zuwa.
“Wannan ba shine ƙarshen labarin Super Falcons ba,” in ji Ajibade a shafinta na X. “Za mu koma bakin aiki, za mu sake sabon tsari. Za mu dawo da ƙarfin mu, saboda haka muke.”
