Shugaban Zambia, Hakainde Hichilema, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon da ya gabata, inda ya samu kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da aka kada, kamar yadda Hukumar Zaɓe ta ƙasar ta sanar a ranar Talata.
Zaɓen da aka gudanar ranar Alhamis a ƙasar Zambia mai arzikin tagulla ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wani gagarumin hargitsi ba.
Da take bayyana sakamkon zaben Shugabar Hukumar Zaɓe ta Zambia, Mwangala Zaloumis tace Hichilema ya lashe zaben bayan samun gagarumin rinjaye a ƙuri’un da aka kaɗa, inda ya samu kashi sittin cikin ɗari.
- Kamfanin jiragen saman Somaliya na shirin farfado da ayyukan sa bayan dogon suma
- Zambiya: Hichilema na kan gaba a sakamakon farko
- Iran ta saka lada dala 30,000 kan kama ko kashe sojan Amurka
Rahotanni na nuna cewa akwai wasu mazbu guda biyar da ba a kaammala ƙidayar ƙuri’unsu ba cikin mazabu 226. To amma Zaloumis tace hakan ba zai shafi sakamakon zaben ba.
Hichilema, mai shekaru 64, ya fitar da wata sanarwa bayan samun nasarar zaɓen, inda ya ce: “Munyi matukar farin ciki saboda amincewar da kuka sanya a hannunmu.”
Ya kuma shaida wa waɗanda suka goyi bayan abokan hamayyarsa cewar “Mun ji ku, kuma za mu ci gaba da yi muku aiki.”
Tuni dai ɗaruruwan magoya bayansa sanye da jajayen kayan jam’iyyar sa ta UPND suka fito kan titunan babban birnin ƙasar, Lusaka, suna rera waƙoƙi da rawa domin murnar nasarar, tare da kunna abubuwan fashewa na murna.
Hakainde Hichilema ɗan shekaru 64 ya kasance ɗan kasuwa, manomi kuma ɗan siyasar Zambia. Shi ne Shugaban Zambia na bakwai kuma na yanzu, ya fara zama shugaban ƙasa ne daga ranar 24 ga Agusta, 2021.
Hichilema ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa sau biyar a baya, a shekarun 2006, 2008, 2011, 2015 da 2016, kafin daga bisani ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2021.
A zaɓen shugaban ƙasa na 2026, an sake zaɓar Hichilema domin ya yi wa’adi na biyu.
Tun daga shekarar 2006, Hichilema ke jagorantar jam’iyyar UPND, bayan rasuwar wanda ya kafa jam’iyyar, Anderson Mazoka.
Kafin ya zama shugaban ƙasa, Hichilema ya kasance babban abokin hamayyar Edgar Lungu, wanda ya kasance shugaban Zambia daga 2015 zuwa 2021.
A ranar 11 ga Afrilu, 2017, an kama Hichilema tare da tuhumar shi da laifin cin amanar ƙasa.
A ranar 16 ga Agusta, 2017, an saki Hichilema daga gidan yari, sannan aka janye tuhumar cin amanar ƙasar da ake yi masa.