Gwamnatin kasar Somaliya ta kammala dukkan shirye-shiryen sake kaddamar da tsohon kamfanin jiragen saman ta na kasa, Somali Airlines a watan Satumba mai zuwa.

Babban Daraktan Hukumar kula da Harkokin Jiragen sama na Somalia (SCAA), Ahmed Moallin Hassan ne ya sanar da matakin, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a babban birnin kasar Mogadishu.

Moallin Hassan ya tabbatar da cewa shirye-shirye sun rigaya sun yi nisa kuma ana sa ran tashin jirgin farko a cikin watan na Satumba.

Tsohon kamfanin na Somali Airlines, wanda aka fi sani da “White Star” ya kasance babbar alama da ke haɗa kasar da manyan biranen Afirka, Turai, da kuma Gabas Tsakiya kafin rushewar gwamnatin Shugaba Siad Barre.

Ana kyautata zaton kamfanin zai fara da jirage biyar, wanda a cikin watan Yulin 2025, Ministan Sufuri Mohamed Farah ya tabbatar da sayen jiragen kirar Airbus A320.

Kawo yanzu, hukumomi a Mogadishu ba su bayyana cikakken tsarin gudanarwa, takamaiman hanyoyin da jiragen za su fara bi, ko tsarin mallakar kamfanin ba.

Sake kaddamar da kamfanin wani bangare ne na nasarorin da Somaliyaa ke samu, tun bayan shekarar 2018, da kasar ta karbe cikakken ikon sarrafa sararin samaniyar ta bayan da aka shafe shekaru da dama ana gudanar da shi daga wajen kasar.

Hukumar SCAA ta zuba jarin kimanin dala miliyan 25 wajen sayen na’urorin na’urori na zamani, sabuntawa da gina hasumiyoyin sadarwa, tsarin sa ido domin inganta tsaro da faɗada iko da sararin samaniyar kasar gaba ɗaya.

Yau kimanin shekaru 35 bayan rushewar ayyukan kamfanin sakamakon yakin basasar da ya daidaita kasar a shekarar 1991, yakain da ya haddasa mata mummunan koma baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *