Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye, bisa zargin kwaikwayon jami’in hukumar da kuma amfani da bindiga ta bogi wajen tsoratar da masu ababen hawa da karɓar kuɗi a Abuja.

An kama Maiye a maboyarsa da ke kusa da NITEL Junction, kan titin Adetokunbo Ademola, Wuse II, bayan hukumar ta samu sahihan bayanan sirri.

A lokacin kama shi, an ce mutumin na sanye da kayan jami’an DSS, sannan yana ɗauke da bindiga ta bogi.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Maiye, wanda ya ce ya fito daga ƙauyen Agbajojun da ke ƙaramar hukumar Mopamuro ta jihar Kogi, ya yi ikirarin cewa ɗan’uwansa mai suna Monday Maiye jami’in DSS ne da ya rasu shekaru da dama da suka gabata.

A cewar wanda ake zargin, kayan DSS da sauran abubuwan da aka samu a hannunsa mallakin ɗan’uwansa ne da ya rasu.

Sai dai DSS na ci gaba da bincike domin gano yadda Maiye ya samu kayan hukumar, da kuma ko akwai wasu mutane da ke da hannu wajen samar masa da kayan.

Hukumar na kuma binciken tsawon lokacin da ake zargin ya shafe yana kwaikwayon jami’an tsaro, da kuma ko ya taba amfani da kayan wajen aikata wasu laifuka.

Maiye na ci gaba da kasancewa a hannun DSS yayin da ake zurfafa bincike kan lamarin.

Kama mutumin ya sake jawo hankali kan matsalar masu sojan gona, musamman waɗanda ke amfani da kayan hukumomin tsaro wajen tsoratar da jama’a, karɓar kuɗi ko aikata wasu laifuka.

Hukumar na jan hankalin al’umma suyi taka-tsantsan a duk lokacin da wani mai ikirarin shi jami’in tsaro ne ya nemi kuɗi ko ya tsoratar dasu, domin kai rahoto ga hukuma mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *