Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya ƙaddamar da Rahoton Binciken Gidaje (GHS) na jihar, domin ƙarfafa tsara manufofi bisa sahihan bayanai da kuma inganta ayyukan da ake samarwa al’umma.
Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Alhaji Faruq Jobe, ya wakilta, ya ce binciken ya samar da cikakkun bayanai kan gidaje daga dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
A cewarsa, rahoton ya ƙunshi kundin tsare-tsare guda biyar da suka hada da bayanai kan jin daɗin iyalai da talauci da aikin yi da hanyoyin samun abin rayuwa da noma da ilimi da kiwon lafiya da gidaje da samar da ruwa.
- Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da sace wasu masu ibada a Ƙaramar Hukumar Borgu
- Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun ceto wani da akai garkuwa da shi, sun kuma dakile harin ’yan ta’adda
- Ba za a iya haɗa baki da almajiri a yi wa mutane fashi ba – Martanin Imam Abdullahi ga ‘Yan Sanda
Ya ce binciken zai taimaka wa gwamnati ta daina dogaro da zato wajen tsara shirye-shiryen ci gaba; maimakon haka ta dogara da sahihan bayanai da kuma ainihin bukatun jama’a.
Radda ya bayyana rahoton a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin gwamnatinsa wajen kafa tsarin gudanar da mulki bisa bayanai da ƙarfafa tsarin kididdiga a fadin jihar.
Ya ce ana sa ran kowace Ma’aikata da Hukuma da Sashen gwamnati (MDAs) za ta yi amfani da bayanan kididdiga wajen tsara manufofi da kasafin kuɗin shekara da kuma tsarin bibiyar ayyuka.
Gwamnan ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa Hukumar Kididdiga ta Jihar Katsina, domin samar da sahihan bayanai masu inganci cikin lokaci, waɗanda za su kasance masu kwatankwacin na ƙasashen duniya, domin inganta tsare-tsare da yanke shawara.
Ya ce ingantattun bayanan kididdiga kayan jama’a ne da ke ƙara gaskiya da riƙon amana da yarda da gwamnati, tare da bai wa masu zuba jari sahihan bayanai kan damar kasuwanci da abubuwan da za su iya bunƙasa a jihar.
Gwamna Radda ya ce binciken wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun dogara ne kan hujjoji, cikakken bincike da kuma shawarwari daga masu ruwa da tsaki.