Brighton ta fara kakar Premier League ta 2026/27 da gagarumar nasara, bayan ta ragargaji Aston Villa da ci 4–0, yayin da Manchester City ta sha da kyar da ci 2–1 a hannun Bournemouth.

A wasan Brighton da Aston Villa, Victor Lindelöf ne ya ci ƙwallar farko ta hanyar kuskuren kai ƙwallo cikin ragar kungiyarsa, kafin Maxim De Cuyper ya ƙara ta biyu.

Daga nan ne Jack Hinshelwood ya zura ƙwallaye biyu, wanda ya nuna rashin nasarar Aston Villa tun farkon rabin lokacin wasar

Villa ta ƙara shiga matsala bayan João Gomes ya karɓi jan kati, lamarin da ya sa aikin dawo da wasa ya ƙara mata wahala.

A Etihad Stadium kuwa, Bournemouth ce ta fara cin ƙwallo, inda Marcus Tavernier ya jefa ƙwallon a minti na 26 bayan an samu matsala a bayan tsaron City.

Manchester City ta matsa lamba domin neman ramuwa, amma ta kasa cin ƙwallo har zuwa kusan ƙarshen wasan.

Sai dai a minti na 85, Marc Guéhi ya farke wa Manchester City da kai bayan bugun corner da Rayan Cherki ya yi.

Lokacin da ake ganin wasan zai ƙare da kunnen doki, Joško Gvardiol ya zura ƙwallar nasara a lokacin ƙarin lokaci, inda Manchester City ta samu maki uku cikin mawuyacin hali.

Wadannan sakamakon sun ƙara nuna cewa kakar Premier League ta bana ta fara da mamaki da kuma wani abu mai kama da wasan kwaikwayo tun daga makon farko.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *