Kotun Koli ta yanke hukunci game da rikicin shugabancin jam’iyyar (ADC), inda ta soke umurnin nan na “status quo antebellum” da aka bayar a baya.
Wannan hukunci ya ba da damar mayar da ragamar shugabancin jam’iyyar hannun Sanata David Mark, yayin da ake ci gaba da shari’ar da ke gaban babbar kotun Tarayya tsakanin tsaginsa da na Nafiu Bala Gombe.
Wannan babban sauyi ne ga makomar jam’iyyar, musamman ganin yadda babban zaben shekarar 2027 ke dada karatowa, wanda yanzu haka ya rage kusan watanni takwas kacal a gudanar da shi.
Maido da Shugabancin David Mark zai ci gaba da tafiyar da al’amuran jam’iyyar a matsayin halattattun shugabanni har sai an kammala shari’ar farko.
Kotun Koli ta fayyace cewa wannan mataki bai kawo karshen karar da ke gaban babbar kotun tarayya ba, kawai an daidaita batun shugabancin ne na wucin gadi.
Ana sa ran wannan hukunci zai kawo karshen dambarwar da ta dabaibaye jam’iyyar, wanda zai ba ta damar mayar da hankali ga tunkarar zabuka masu gabatowa.
Yayin da mambobin jam’iyyar ke jiran fitowar cikakken bayanin hukuncin daga alkalai, masana shari’a na ganin wannan mataki a matsayin mai muhimmancin bin ka’idojin gudanarwa na cikin gida kafin tsoma baki daga kotu.
Da yake fashin baki kan abin da ya faru a yau, Barrister Robort Emekunu SAN, yace kawo yanzu kotun tayi watsi ne da bukatu 6 daga cikin 7, da suka gabatar mata game da shugabancin jam iyyar karkashin David Mark.
Abin jira a gani shine hukuncin da kotun karshe zata dauka zata yanke akan wadannan shari’o’i.
