Masana’antar kade kade a kasar Ostireliya (ARIA), ta fito da wata sabuwar dokar da zata haramtawa wakokin da akayi amfani da fasahar (AI) wajen hadawa ko ingantawa, shiga gasar jerin fitattun wakokin gida, ko samun damar tsayawa takara a bana.

Matakin ya biyo bayan yamadidin da ya barke, bayan sake sarrafa wata wakar fitacciyar mawakiya Madonna mai suna “Like a Prayer”.

Tunda farko, wani makadi mai suna Josh Fawaz ne ya fitar da wakar, bayan sauya mata muryoyi da salon kidan ganga, ta hanyar fasahar AI.

Salon da makadi Fawaz yayi amfani dashi, ya sanya wakar mamaye saman teburin wakoki 20 mafi shahara a kasar Ostrileya, in da masu sauraro sama da miliyan 48 suka saurari wakar a shafin sauraron wakoki na Spotify.

Duk da korafe-korafe daga masu sha’awar kade kade, ARIA ta sanar da cewa daga ranar Juma’a mai zuwa, wakokin da aka yi amfani da fasahar AI wajen rerawa da rubutawa ba za su sake samun gurbi a jerin fitattun wakokin kasar ba.

ARIA, ta yi Karin bayanin cewar, wakokin da aka yi amfani da fasahar AI wajen ingantawa ta fuskar kida ko muryar Dan adam ne kadai, za su ci gaba da samun gurbin shiga cikin teburin  fitattun wakoki, har ma su iya kaiwa ga nasarar samun kyautattuka.

Daraktar gudanarwa ta ARIA, Annabelle Herd, ta bayyana cewa duk da cewa masana’antar kade-kaden kasar na bukatar tafiya da zamani, bai kamata a rika amincewa da wakokin da aka saci basirar wadanda suka rera su na ainihi ba.

Masu ruwa da tsaki a bangarorin biyu sunyi maraba da matakin, tare da jaddada goyon bayan su ga kokarin kare hakkin mallaka, daga mamayar masu kokarin satar basirar mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *