Akalla mutane 270 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da sama da 1,300 suka bace, bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da ta afku a kan iyakar Nepal da Tibet.
Lamarin ya afku ne ranar Laraba, bayan wani bangare na kankara ya zaftare daga tsaunukan Himalayas dake kudu da nahiyar Asiya, lamarin da ya janyo kwararar ruwa, laka da duwatsu mai matukar karfi zuwa kogunan da ke yankin.
Ambaliyar ta mamaye kauyuka da garuruwa, tare da lalata gidaje, hanyoyi, gadoji da wasu muhimman ababen more rayuwa.
A Nepal kadai, hukumomin kasar sun ce mutane 826 har yanzu ba a san inda suke ba, ciki har da akalla ’yan yawon bude ido 579, wadanda suka hada da ’yan Nepal da baki daga kasashe daban-daban.
Hukumomin kasar sun kuma ce gawarwaki 165 sun riga sun dawo hannun jami’an ceto a wasu yankunan da ambaliyar ta fi kamari.
A bangaren Tibet na kasar Sin kuwa, hukumomi sun ce mutum uku sun mutu, yayin da wasu 558 suka bace, ciki har da baki 260, wannan ya sa adadin mutanen da suka bace a bangarorin biyu ya haura 1,300.
Rahotanni sun ce yankin Rasuwa da ke arewacin Nepal na daga cikin wuraren da bala’in ya fi kamari, inda tumbatsar manyan kogunan Bhote Koshi da Trishuli ya janyo cikar kananan koguna a gundumomi dake kudancin kasar.

A wasu wuraren, guguwa da laka sun tafi da kanana da manyan motoci da gine-gine, kamar yadda wani faifan bidiyo aje yadawa ya nuna mutane suna gudun tsira, yayin da wata guguwa hade da ruwa da tarkace ke kutsawa cikin garuruwan dake kan iyakar Nepal da Tibet.
- Mummunar ambaliyar ruwa ta halaka mutum 12 Accra
-
Ambaliya: NEMA ta bukaci a fara kwashe jama’a yayin da ruwan sama ke ƙaruwa
-
Toshewar hanyoyin ruwa na ƙara ta’azzara matsalar ambaliya a Abuja
Bala’in ya kuma jefa iyalan wadanda suka bace cikin rudani, yayin da suke zagaya asibitoci da ofisoshin ‘yan sanda domin neman labarin ’yan uwansu. Wasu daga cikin wadanda suka bace sun hada da mazauna yankin, jami’an tsaro, mahajjata da kuma ’yan yawon bude ido da ke ziyartar yankin na Himalaya.
Hukumomin Nepal sun ce jami’an ceto na amfani da jirage masu saukar ungulu wajen kai dauki da kuma neman wadanda suka tsira a wuraren da hanyoyi da gadoji suka lalace. Akalla mutane 123, ciki har da ’yan Nepal 94 da baki 29, aka yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen ceto su a yankunan Timure.
Ambaliyar ta kuma lalata akalla gadojin mota 35, da na tsallakawa 45 da kusan kilomita 40 na hanyoyi, lamarin da ya kara haifar da tsaiko a ayyukan ceto da kai kayan agaji ga wadanda bala’in ya shafa.

Masana sun yi gargadin cewa dumamar yanayi na kara sanya kankarar dake tsaunukan Himalaya cigaba da narkewa, wanda zai iya kara hadarin samun irin wadannan bala’o’i a yankunan da ke kusa da koguna da tsaunuka.
A halin yanzu, ayyukan neman wadanda suka bace da ceto wadanda suka makale na ci gaba a Nepal da Tibet, yayin da hukumomi ke tattara karin bayanai kan adadin wadanda suka mutu, ko suka bace da kuma girman barnar da ambaliyar ta haifar.