Marigayi Saleh Shehu Ashaka yayi shura a shirye shiryen rediyo na VAO Hausa.

Al’ummar Musulmi da ma duniyar aikin jarida sun tashi da labarin rasuwar fitaccen ɗan jaridar nan da ya dade yana aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), Saleh Shehu Ashaka.  Ya rasu ne a birnin Alƙahira na kasar Masar, bayan rashin lafiya.

An gudanar da jana’izarsa a Masallacin Husari da ke birnin Alƙahira. A hannu guda kuma, iyalai da abokan arziki a birnin Kano sun gudanar da Sallar Ga’ibi (Salat al-Ghaib) a gidan su, da ke unguwar Farm Center bayan sallar Azahar.

Hoto: Affajo Abdussalam Tsanyawa.

A yanzu haka an fara zaman karɓar gaisuwa a gidan mahaifin sa Alhaji Shehu Ashaka, inda abokan aiki da ma waɗanda ba ƴan jarida ba, ke tururuwa domin mika saƙon ta’aziyyar su.

Tuni sakonnin ta’aziyya suka cika  kafofin sada zumunta daga tsoffin abokan aikinsa na (VOA) da sauran gidajen rediyo na duniya. Suna bayyana shi a matsayin Mai hazaƙa.

Muna mika ta’aziyyar mu ga iyalai da daukacin abokan marigayin, Allah ya jikansa da rahama.

Wannan tsari ya yi daidai da mizanin aikin jarida na zamani (Mojo da Digital Publishing). Allah ya jikan Saleh Shehu Ashaka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *