Dole ne mu tashi tsaye domin yaki da labaran karya. Hoto: Adnan Suleiman

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai, hukumomin gwamnati, da masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin yaƙi da yaɗa labaran karya da gurbatattun bayanai.

Da yake jawabi a ranar Litinin a Abuja yayin taron tunawa da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya na shekarar 2026, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Mohammed Idris, ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanya batun hadin gwiwa da kafafen yaɗa labarai akan gaba.

Ya kara da cewa ‘yancin ‘yan jarida babban hakki ne da kundin tsarin mulki ya amince da shi, kuma gwamnati ta kuduri aniyar samar da yanayi mai kyau inda kafafen yaɗa labarai za su yi aiki cikin aminci da bin doka da oda.

“Wannan gwamnati ta ba da muhimmanci ga hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa don inganta aikin jarida da kuma yaki da labaran karya.” Inji shi

Mohammed Idris ya nanata cewa wasu daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka don tabbatar da gaskiya sun hadar da bayar da damar samun bayanai, ƙarƙashin dokar nan ta ƴancin samun bayanai (FOI).

Baya ga bayar da damar zuba jari a fannin sadarwa na gwamnati, da ƙulla alaka da hukumar UNESCO don kafa cibiyar horarwa kan dabarun sanin makamar aiki ta (IMILI) a Abuja.

A ƙarshe, Ministan ya bukaci ‘yan jarida da su kasance masu kwarewa, adalci, da bin ka’idodin aikin su, da nuna kishin kasa da gaskiya.

Hukumar raya al’adu, ilmi da kimiyya ta Majalisar dinkin duniya UNESCO ce ta ware kowacce ranar 3 ga watan Mayun kowacce shekara a matsayin ranar ‘yancin yan jarida ta duniya, shekaru 35 da suka wuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *