Jam iyyar PDP ta gudanar da taron majalisar zartaswa karo na 103

Kashi biyu bisa uku na shugabannin tsagin jam’iyyar PDP sun amince da nadin Kabiru Tanimu Turaki ya jagoranci Kwamitin Gudanarwa na riƙon kwarya yayin taron Majalisar Zartarwarsu karo na 103 a Abuja.

Bayan amincewa da nadin, nan take aka rantsar da Kabiru Tanimu Turaki tare da sauran mutane tara da za su rike mukamai daban-daban, domin taimaka mata zuwa babban zabe.

A karshen taron, jam iyyar ta fitar da jadawalin yadda za ta tunkari babban zabe, inda ta bayyana Litinin 5 zuwa Laraba 13 ga watan Mayu domin fara sayar da fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara ta Shugaban Kasa da Gwamna da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki ta Jiha.

Sai ranakun Juma’a 15 zuwa Litin 18 ga watan Mayu a matsayin ranakun tantance dukkanin ‘yan takara, yayin da ranar 22 ga watan na Mayu za ta kasance ranar wallafa sunayen wadanda suka tsallake tantancewa.

Ranar 28 ga wata ne jam iyyar zata gudanar da zabukan fidda gwani a guraben da ba’a samu masalaha ba, yayin da bababn taron jam iyyar zai kasance ranar 30 ga watan Mayu. Inda anan zaa tabbatar da sakamakon zaben dan takarar Shugaban Kasa. kamar yadda yake kunshe cikin samarwar da sakataren yada labaran jam iyyar Honarabul Theophilus Dakas Shan ya fitar.

Sai dai masharhanta na ganin zai yi walaha PDP ta shiga zaben bana, idan akayi la’akari da hukuncin kotun daukaka kara da ya haramta babban taron Badin, da kuma wata kotun da ta baiwa bangaren Wike damar gudanar da babban taro da ya baiwa Anyanwu nasarar zama shugaban jam’ iyya.

A ƙarshen watan Aprilun shekarar 2026 ne Kotun Koli ta haramta taron da jam’iyyar ta yi a birnin Badun, hukuncin da ya haramta duk abin da akayi ciki harda zaɓen Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *