Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, martani kan alƙawarinsa na cewa zai “sake buɗe iyakokin Najeriya” idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, tana mai cewa tuni iyakokin ƙasar suke a buɗe.

Fadar Shugaban Ƙasar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwar, Sunday Dare, ya fitar ranar Juma’a mai taken “Atiku da Iyakoki: ’Yan Najeriya Sun Cancanci Gaskiya, Ba Taken Kamfen Ba.”

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, gwamnatin tarayya ta sake buɗe mafi yawan iyakokin ƙasar a ranar 14 ga Maris, 2024, kuma tun daga lokacin ba ta sauya wannan matsaya ba.

Ta ƙara da cewa: “Saboda haka yana da wuya a fahimci waɗanne iyakoki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa yake nufin zai ‘buɗe’, alhali iyakokin a buɗe suke.

A ranar 14 ga Fabrairu, 2026, Shugaba Tinubu ya buɗe iyakar Kamba da ke Jihar Kebbi, lamarin da ya haifar da moriyar tattalin arziki da diflomasiyya.”

Fadar Shugaban Ƙasar ta ce idan Atiku yana nufin sassauta wasu daga cikin matakan kula da iyakokin da ake da su, to ya kamata ya bayyana wa ’yan Najeriya takamaiman matakan da yake son cirewa da kuma irin matakan tsaron da gwamnatinsa za ta ɗauka.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, ingantaccen tsarin kula da iyakoki yana buƙatar haɗin gwiwar hukumomin shige da fice da ta fasa kwairi da musayar bayanan sirri da sa ido da amfani da fasaha da kuma haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro.

Ta ce batun yana da muhimmanci musamman saboda yanayin tsaron Najeriya da kuma alaƙarta da abubuwan da ke faruwa a yankin Sahel da Tafkin Chadi (Lake Chad Basin).

Sanarwar ta ce Najeriya tana da iyaka da Nijar da Chadi da Kamaru, kuma yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da manyan laifuffukan da suka ratsa iyakokin ƙasashe, raunin kula da iyakoki na iya zama hanyar da masu aikata laifuka ke amfani da ita wajen shiga wasu ƙasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *