Wata kotu dake Dutsen – Alhaji yankin babban birnin tarayya Abuja ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin zaman a kwanaki 250 a gidan gyaran hali bisa samunsu da laifin mallakar alburusai ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ce ta kama mutanen bayan samun wasu bayanan sirri.
- Iyakokin Najeriya a buɗe suke, Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar wa Atiku martani
- Abin da ya kamata ku sani game da sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- Zan dawo da kasashen AES cikin Ecowas – Atiku
Cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sanda ta FCT, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce an kama Yau Sule da Mariya Sule ne a ranar 2 ga Yuni, 2026 a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, bayan jami’an ’yan sanda sun samu bayanan sirri da suka danganta shi da safarar alburusai zuwa ga masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka da ke aiki a yankin Arewa ta Tsakiya da Babban Birnin Tarayya.
A yayin samamen, jami’an ’yan sanda sun kwato alburusai 81 masu rai na 7.62mm na AK-47, da kuma alburusai 100 masu bel na 7.62mm waɗanda ake amfani da su a bindigar General Purpose Machine Gun (GPMG).
Kotun ta same su da laifin mallakar alburusai masu rai ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar Makamai ta Ƙasa (Firearms Act), inda ta yanke musu hukuncin ɗaurin kwanaki 250 kowannensu, ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Tuni dai aka tura su gidan gyaran hali na Suleja domin tabbatar da hukuncin.