Dakarun Operation Hadin Kai sun dakile wani harin ’yan ta’adda da aka kai wa sansanin sojoji a garin Kukawa na Jihar Borno, inda suka hallaka ’yan ta’adda da dama tare da lalata babura 10 da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:50 na dare ranar 28 ga Agusta, 2026, lokacin da ’yan ta’adda suka kai hari kan dakarun 101 Special Forces Battalion da aka jibge a Kukawa.
A cewar wani rahoto da shalkwatar tsaro ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook, dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa ta hanyar harbe-harbe kai tsaye, inda suka samu nasarar fatattakar maharan tare da tilasta musu ja da baya zuwa yankin Cross Kauwa.
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya tafi Angola don halartar taron AU
- Sojoji sun kama masu taimaka wa ’yan ta’adda 3, sun lalata maboyarsu a Kaduna da Katsina
- Tinubu ya shigar da ƙara kotun Amurka don hana fitar da takardun zargin safarar miyagun ƙwayoyi
A yayin musayar wuta, an hallaka wasu daga cikin ’yan ta’addan, yayin da wasu suka samu raunukan harbin bindiga kafin su tsere daga yankin.
Bayan artabun, dakarun sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano gawarwakin wasu daga cikin ’yan ta’addan, abin da ya tabbatar da asarar da maharan suka yi.
Yayin da ’yan ta’addan ke kokarin tserewa zuwa Cross Kauwa a kan babura, rundunar sama ta Operation Hadin Kai ta shiga aikin dakile musu hanya.
Jiragen saman sojojin sun kai hari kan wasu ’yan ta’adda da suka fake a ƙarƙashin bishiyoyi, inda aka kiyasta cewa an hallaka kimanin ’yan ta’adda 10.
Bayan haka, na’urorin leƙen asiri, sa ido da gano abokan gaba (MNJTF) sun bibiyi wasu babura kusan 20 da ke ɗauke da ’yan ta’adda da ke gudu zuwa yankin Tunbuns/Kangarwa.
Bayan samun bayanan sirrin, rundunar sama ta kai wani sabon samamen da aka tsara daidai kan ’yan ta’addan.
A wannan samamen, an hallaka ƙarin ’yan ta’adda 15, yayin da aka lalata babura 10, wanda ya ƙara rage musu damar zirga-zirga da kuma ƙarfin gudanar da hare-hare.
Nasarar ta zo ne sakamakon haɗin gwiwar dakarun ƙasa da rundunar sama, inda aka samu nasarar dakile harin tare da hana ’yan ta’addan samun damar tserewa cikin sauƙi.