Mai riƙe da kofin Gasar Ƙwararrun Ƙwallon Ƙafar Firimiyar Najeriya (NPFL) Enugu Rangers ta buɗe wasan kakan bana ta 2026/27 da buga canjaras ci 1-1 tsakaninta da Katsina United a wasan da suka buga a ranar Lahadi, a filin wasa na MKO Abiola, dake Abeokuta.

Da farko, ƙwallon da Luis Dadon ya ci a minti na 35 ne ta ɗora Katsina United akan gaba har aka kusan tashiwa a wasan.

Sai dai mai riƙe da kofin na bara, Rangers ta ƙara ƙaimi wajen matsa lamba har sai da ta farke ƙwallon da aka zura mata a minti na 907 ta hannun Chibueze Oputa.

A wani wasan na daban, Kwara United ta tashi ci 2-2 da Kano Pillars a garin Ilorin a wasan da suka buga a ranar Lahadi.

Abdulraheem Shola da kuma Rabiu Ali sune suka ci wa kungiyoyin kwallayen a bugun daga kai Sai mai tsaron gida yayin fafatawar a mintina na 13 da kuma 30.

Daga baya, mai masaukin baƙi, Kwara United ta farke ƙwallayenta ne ta hannun ɗan wasa Jerry Alex a mintuna na 47 da kuma 905.

Ga sakamakon wasannin da aka buga gaba daya kamar haka:

Barau 3-1 Nasarawa United

Bendel Insurance 2-1 Warri Wolves FC

Enugu Rangers 1-1 Katsina United

Ikorodu City 3-1 Ranchers Bees

Kwara United 2-2 Kano Pillars

Niger Tornadoes 2-1 Enyimba

Rivers United 2-0 Plateau United

Doma United 2-0 Sporting Lagos

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *