Bankin duniya yace tattalin arzikin ƙasashen Afirika zai bunkasa, idan kasashen da ke cinikayya da juna su ka matsa kaimi amfani da damar harkokin cinakayya a tsakani, karkashin tsarin nan na kasuwancin baya AfCFTA.

Wani rahoto da bankin ya fitar kan makomar bunkasar cinikayya da tattalin arzikin nahiyar, yace duk da cewa Afirka na yin ciniki da yawa idan aka kwatanta da girman tattalin arzikinta, har yanzu yawancin abin da take fitarwa bai wuce albarkatun ƙasa zuwa ƙasashen waje ba.

Rahoton ya ce cinikayyar da ake yi tsakanin ƙasashen Afirika na matakin kaso sha-biyar zuwa ashirin cikin ɗari na jimillar cinikin nahiyar.

Ya ce tsarin na cinikayya a cikin Afirika wato AfCFTA ya fi kasancewa mai bambancin kayayyaki kuma yana da alaƙa da masana’antu fiye da cinikin da nahiyar ke yi da sauran sassan duniya.

Masu binciken sun ce haɗa tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ba wani zaɓi ba ne kawai, sai dai muhimmin mataki ne wajen bunƙasa masana’antu. Rahoton ya ce idan ƙasashe suka haɗa ƙarfin samar da kayayyaki a matakin yanki, za a iya samar da masana’antun da daidaikun ƙasashe ba za su iya kafawa da kansu ba.

Rahoton ya kuma nuna cewa matsalolin da ke kawo cikas ga ciniki ba su tsaya kan iyakokin ƙasashe ba. Rashin ingancin kwastam, bambancin dokoki da ƙa’idoji, da kuma raunin hanyoyin sufuri da kayan more rayuwa na ƙara tsadar ciniki. Don haka rahoton ya ce haɗa tsarin kayayyaki, bayanai, kuɗi da dokoki yadda za su yi aiki ba tare da cikas ba ya fi muhimmanci fiye da rage haraji kawai.

Rahoton ya yi kira da a ƙarfafa aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA, wato yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na Afirika. Ya ce yarjejeniyoyin da ke da cikakkun tanade-tanade kuma masu tilasta bin doka na haifar da fa’ida mai yawa ga ciniki da tattalin arziƙi fiye da yarjejeniyoyin da ba su da ƙarfi.

Haka kuma, rahoton ya ce Afirika na buƙatar ƙarin saka hannun jari a abubuwan da za su amfani dukkan ƙasashe, ciki har da hanyoyin sufuri, makamashi, dandamalin dijital da tsaro. Ya ce samun ingantattun waɗannan abubuwa na daga cikin muhimman sharuddan da za su ba da damar ciniki da samar da kayayyaki su gudana cikin sauƙi tsakanin ƙasashen nahiyar.

Rahoton ya yi gargadin cewa sauye-sauyen tsarin cinikin duniya, raguwar wasu damar shiga kasuwannin ƙasashen waje da kuma sauyin tsarin samar da kayayyaki a duniya na sake fasalta makomar tattalin arzikin Afirika.

Ya ce nahiyar na buƙatar wucewa daga matakin rattaba hannu kan yarjejeniyoyi zuwa samar da ingantaccen tsarin haɗin kan tattalin arziƙi da zai ƙara samar da masana’antu, ayyukan yi da ci gaban kasuwanci a Afirika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *