Mahukuntan birnin Pattaya da ke Thailand sun tsaurara matakan yaki da karuwanci, yayin da yankin ke shirin karbar bakuncin jirgin ruwan sojin Amurka, bayan shafe sama da kwanaki 200 a cikin teku.

Jirgin ruwan sojin Amurkan mai suna USS Abraham Lincoln, zai isa birnin Pattaya a ranar Laraba, tare da wasu jiragen ruwa biyu na rundunar, inda jirgin da jami’an sojin Amurkan su dubu biyar za su yada zango domin samun damar hutawa.

Jirgin yakin Amurka kenan yake tashi daga kan jirgin ruwan Abraham Lincoln [Hoto:Reuters]
Rahotanni na cewa jami’an tsaro a Pattaya, sun ce zasu kara yawan jami’ai a gabar tekun da jirgin zai tsaya, da kuma wuraren shakatawar dare.

Hakan na zuwa ne bayan wani samame da aka gudanar a karshen mako, inda aka kama karuwai 50 dake gararamba a manyan tituna da wuraren shakatawa na bakin ruwan.

Koda yake, Shugaban ‘yan sandan Pattaya, Anek Srathongyoo, ya ce zasu iya fuskantar kalubale wajen dakile karuwancin, saboda masu wannan sana’a na iya neman kwastomomi a inda jama’a ke taruwa ba tare da jami’an tsaro sun sani ba.

Karuwanci haramun ne a Thailand, sai dai harkar na ci gaba da bunkasa a wasu manyan wuraren yawon bude ido, ciki har da Bangkok da Pattaya.

Ziyarar jirgin ruwan Amurkan na daukar hankalin hukumomi saboda ana sa ran bunkasar tattalin arzikin yankin na wani dan lokaci.

Magajin birnin Pattaya, Poramase Ngampiches, ya ce kowane sojan Amurka na iya kashe tsakanin baht 1,000 zuwa 3,000 a rana, kwatankwacin dala 30 zuwa 91, gwargwadon tsawon lokacin da zai shafe a birnin.

Sai dai masana harkokin yawon bude ido sun yi gargadin cewa karuwar masu yawon bude ido na iya kara hadarin cin zarafin masu sana’ar karuwancin, da kuma yaduwar cututtukan da ake dauka ta hanyar saduwa.

Wani Masani a tsangayar koyar da aiki a bangaren yawon bude ido na Jami’ar Bangkok mai suna Pipatpong Fakfare, ya nuna damuwa kan rahotannin matsalolin lafiyar kwakwalwa da yunkurin kashe kai da aka ce sun faru tsakanin wasu jami’ai da ke cikin jirgin na Abrahaman Lincoln.

USS Abraham Lincoln ya bar sansanin sa da ke San Diego a watan Nuwamba, kafin daga bisani a karkatar da shi zuwa Gabas ta Tsakiya domin tallafawa ayyukan soji a yakin da Amurka ta gwabza da Iran.

Pattaya dai ta samu gagarumin sauyi daga matsayin karamin kauyen kamun kifi zuwa babbar cibiyar yawon bude ido, musamman sakamakon yawan zuwan sojojin Amurka a lokacin yakin Vietnam.

Shugaban kungiyar yawon bude ido ta Chonburi, Thanet Supornsahasrungsi, ya ce tasirin zuwan sojojin ga tattalin arzikin birnin zai dogara ne da wuraren da za su zabi ziyarta, domin wasu na iya zuwa babban birnin Bangkok maimakon zama a Pattaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *