Amurka da Iran sun cigaba da musayar hare-hare a wani sabon rikici da ake ganin shi ne mafi girma cikin sama da wata guda, lamarin da ya ƙara tayar da fargabar cewa yaƙin na iya yaɗuwa zuwa wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Rundunar Sojin Amurka ta ce ta kai hare-hare kan cibiyoyin soji da dama a gabar tekun kudancin Iran. Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗin cewa Iran za ta fuskanci mummunan hari idan ta mayar da martani.

Iran ta ce hare-haren Amurkan sun shafi wurare da dama, ciki har da wani gida da ake gudanar da bikin aure a birnin Kuhestak cikin Lardin Hormozgan da ke kudu maso gabashin Iran.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta ce an kashe aƙalla mutum huɗu, yayin da fiye da mutane 68, ciki har da mata da yara, suka jikkata.

Rahotanni daga Iran sun tabbatar da jin fashewar abubuwa a wasu garuruwan bakin teku, hare-haren makamai masu linzami sun kashe mutane bakwai a wurare uku, tare da jikkata wasu takwas, wanda a jimlace, aƙalla mutane 18 ne suka mutu.

Iran ta yi ikirarin cewa hare-haren da ta kai Kuwait sun lalata wasu jirage marasa matuƙa da kuma wani wurin ajiye su, tare da kashe wasu sojojin Amurka,  sai dai Kuwait ta ce ta kakkabo wasu daga ciki, da makamai masu linzami, ba tare da bayar da rahoton asarar rayuka ba.

Hukumomin Jordan su ma sun ce sun kakkabo makamai masu linzami 10 daga cikin 13 da suka shiga sararin samaniyarta, yayin da sauran ukun suka faɗi a wuraren da ba a cika zama ba.

Sabon rikicin ya zo ne a lokacin da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran ta tsaya cak,  Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce Tehran za ta mayar da martani idan Amurka ta koma kan sharuɗɗan yarjejeniyar da ta dakatar da fadan soji.

Jagoran Iran Mojtaba Khamenei, ya ce ƙasar sa ta koyi darussa da ba za ta manta ba, daga maƙiyan su Amurka, inda ya nemi ƙasashen duniya su ɗauki mataki kan hare-haren Amurka.

A nasa ɓangaren, Donald Trump ya ce Amurka ba ta neman tilasta Iran komawa teburin tattaunawa, yana mai cewa Washington yanzu tana da kusan cikakken iko kan mashigar Hormuz.

Masana tsaron teku sun yi gargadin cewa sabbin hare-haren na iya maimaituwa saboda har yanzu ba a warware batun ikon mashigar Hormuz da kuma takaddamar tsakanin ƙasashen biyu ba.

Sai dai Amurka na neman a kawo ƙarshen toshewar mashigar da Iran ke yi ba tare da wasu sharuɗɗa ba, yayin da Tehran ke son Washington ta kawo ƙarshen shingen ruwan da ta sanya wa tashoshin jiragen ruwan Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *