Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun hallaka wasu ’yan ta’adda tare da kama makamai da alburusai masu yawa a wasu hare-hare daban-daban da suka gudanar a jihohin Zamfara da Kaduna.
A wata sanarwa da jami’in watsa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar 2 ga Satumba, 2026, ya bayyana cewa dakarun sun samu nasarar ne bayan gudanar da wasu ayyuka na musamman bisa bayanan sirri.
Ya ce a jihar Zamfara, dakarun Sashe na 2 sun yi wa ’yan ta’adda kwanton bauna a yankin Kwanar Jolof, bayan samun bayanan sirri kan motsinsu daga yankin Fakai zuwa Kwanar Jolof da Tashar Dole da ke ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi.
- INEC na duba yiwuwar gudanar zaɓen shugaban ƙasa na gwaji kafin babban zaɓe
- Ba aikin Dan sanda ba ne hana yawon Shanu a Abuja – CSP Ani Iniedu
- Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara ƙarfi, gwamnati na hasashen zuwa dala tiriliyan ɗaya
A yayin arangamar, sojojin sun hallaka da dama daga cikin ’yan ta’addan, yayin da wasu suka tsere.
Binciken da aka gudanar bayan harin ya sa aka gano makamai da suka haɗa da na’urar harba roka (RPG), rokar RPG guda ɗaya, bindigar AK-47 guda ɗaya, magazinan AK-47 guda shida, harsasai 106 da kuma babur guda ɗaya.
Sanarwar ta ƙara da cewa a jihar Kaduna, dakarun Sashe na 1 sun kama wata mota a wani shingen bincike na gaggawa da ke kan hanyar Saulawa zuwa Zariya.
A yayin binciken motar, wani fasinja ya yi ƙoƙarin hana a duba jakarsa tare da yunƙurin tserewa, lamarin da ya sa sojojin suka bi shi suka kuma kashe shi.
Bayan buɗe jakar, an gano cewa an ɓoye harsasai 793 a cikin garin da ke cikinta.
Rundunar ta ce a halin yanzu motar da direbanta suna hannunta domin ci gaba da bincike.
Operation FANSAN YAMMA ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare domin tarwatsa hanyoyin ’yan ta’adda, dakile safarar makamai da alburusai, da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da matsalar tsaro ta shafa.