Yayin da ake tunkarar babban zaɓen Najeriya na 2027, wasu ‘yan siyasa da masu rajin kare dimokuraɗiyya sun nuna damuwa kan sahihancin zaɓen.
Sun yi gargadin cewa maguɗi, barazana, tashin hankali da raunin wasu hukumomin da ke kula da zaɓe na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓen.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Peter Obi, ya ce magoya bayansa ba za su sake bari a tsoratar da su ko hana a ƙirga ƙuri’unsu ba.
Yayin wani taron tattaunawa da yan-dangwale a Fatakwal, ya ce zaɓen 2027 zai wuyar maguɗi fiye da yadda aka gani a 2023, yayi kira ga ‘yan Najeriya su kare ƙuri’unsu a rumfunan zaɓe.
Duk da Obin ya nuna damuwa kan yiwuwar samun matsala a na’urorin zaben idan akayi la’akari da yadda zabukan suka kasance a baya, yace jam’iyyarsu za ta tanadi hanyoyin magance su domin tabbatar da sahihin zaɓe.
A nasa ɓangaren, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, ya ce Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa mai ƙwarewa da jajircewa wajen magance matsalolin ƙasar. Ya buƙaci masu zaɓe su guji maimaita kura-kuran baya, yana cewa zaɓen 2027 wata dama ce ta zaɓar shugabanci nagari.
Shi ma babban lauyan kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana, ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar wani muhimmin gwaji gabanin zaɓen 2027. Ya yi magana kan barazanar tashin hankali, maguɗin zaɓen fidda gwani, ƙarancin amincewa da tsarin zaɓe da kuma raunin tsarin shari’a, tare da kira ga ‘yan Najeriya su tabbatar da cikakken ‘yancin hukumar zaɓen.
A gefe guda, jam’iyyar ADC ta ce za ta shiga zaɓen 2027 duk da damuwarta kan wasu matakai da ayyukan INEC. Jam’iyyar ta ce za ta kalubalanci duk wani mataki da ta ga ya sabawa doka, tare da yin kira ga INEC ta bayyana dalilin da ya sa aka mayar da wasu jami’an zaɓe a Jihar Ribas da kuma tabbatar da cewa ɗaukar ma’aikatan wucin gadi na zaɓe ba tare da katsalandan ba.