Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, sun nuna damuwa kan zargin da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya yi masa na hannu wajen shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna.
Janar Christopher Musa ya yi wannan zargi ne a ranar 3 ga Satumba, 2026, yayin wata hira kai-tsaye da shirin Politics Today na gidan talbijin na Channels.
Iyalin El-Rufai sun ce an yi wannan zargi mai tsanani ba tare da gabatar da wata shaida da za ta tabbatar faruwan hakan ba.
Sun ce duk da cewa Janar Musa na da damar bayyana ra’ayinsa, su ma suna da hakkin neman a gabatar da sahihiyar hujja da za ta tabbatar da irin wannan zargi mai tsanani.
Iyalan sun ce idan babu wata shaida, suna kira ga Janar Musa da ya fito fili ya janye zargin ta kafar talbijin din da ya yi amfani da ita wajen yin hakan.
A cikin wata sanarwa da Honarabul Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan a Abuja ranar 7 ga Satumba, an bai wa Janar Musa wa’adin kwanaki bakwai daga ranar sanarwar, ko dai ya gabatar da hujjar zargin ko kuma ya janye shi tare da ba da cikakken uzuri a bainar jama’a.
Sanarwar ta ce idan Janar Musa bai yi hakan ba cikin wa’adin da aka kayyade, iyalan El-Rufai za su bi dukkan hanyoyin shari’a da doka ta tanada domin mayar da martani kan zargin da suka bayyana a matsayin wanda ba shi da tushe.