Rundunar ‘Yan sanda ta FCT, a ranar 7 ga Satumba, 2026, da misalin karfe 7:45 na dare, ta sami kiran gaggawa na rahoton ruftuwar wani gini a Titin Abidjan, Wuse Zone 3, Abuja.

Bayan samun rahoton, tawagar jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda na Sashen Ayyuka (ACP), Edward Akaniyene, da Kwamandan Shiyya na Metro (ACP), Georgelyn Ufomadu, sun gaggauta isa wurin da lamarin ya faru.

Wata sanarwa da PPRO na rundunar, SP Josephine Adeh, ta sanyawa hannu ta ce  tawagar, tare da jami’ai daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Hukumar Kare Hadurra ta Kasa (FRSC), Hukumar Kula da Tituna ta Kasa (FERMA), Hukumar Kashe Gobara ta Kasa (FFS), Sashen Tsaro na Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA), da sauran hukumomin agajin gaggawa masu ruwa da tsaki, nan take suka fara aikin ceto da bincike a wurin.

Binciken farko ya nuna cewa a baya ma’aikatar kula da ci gaban birane (Department of Development Control) ta Abuja ta riga ta sanya wa ginin alama kuma ta rufe shi. Kawo yanzu, ba a tabbatar da samun mutanen da suka rasa rayukansu ko jikkata ba.

Sai dai, ana ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto domin gano tare da ceto duk wani wanda zai iya kasancewa a makale a karkashin baraguzan ginin. Za a bayyana ƙarin cikakken bayani kan girman barna a lokacin da ya dace.

Har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano ainihin yanayi da abubuwan da suka haddasa rugujewar ginin.

Rundunar tana kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kuma su kasance masu lura da tsaro, su guji zuwa yankin da abin ya shafa, sannan su ba da hadin kai ga masu aikin ceto domin saukaka aikin da ake yi.

Haka kuma ana shawartar al’umma da su gaggauta rahoton duk wani abu da ba su amince da shi ba ko na gaggawa ga Rundunar ta lambobin gaggawa kamar haka: 08032003913, 08061581938.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *