Mazauna kauyuka a kananan hukumomi uku na Jihar Sokoto na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon tsanantar hare-haren da ke kara yaduwa zuwa yankunan da a baya basu da matsala.
Sabbin hare-haren da aka kai kwanan nan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15, yayin da aka yi garkuwa da wasu mutane kusan 79.
Wadannan sabbin hare-hare sun auku ne a kananan hukumomin Rabah, Isa, da Dange Shuni, kwanaki kadan da kai wasu jerin hare-haren a garuruwan Bodinga, Kebbe, Goronyo, Tureta, da Tambuwal.
A ranar Lahadi da misalin karfe 10 na dare, mahara sun farwa kauyen Tofa inda suka kashe mutane bakwai, ciki har da wata mata da aka yanka danta a gabanta. Sannan an sace Mutane 35, sai dai 8 daga ciki sun kubuta, abin da ya rage adadin wadanda ke hannun maharan zuwa 27.
A kauyen Tidibale da ke karamar hukumar Isa kuwa, maharan sun kai farmaki a ranar Asabar inda suka kashe mutane biyar, suka sace mutane kusan 50, sannan suka kona motocin sojojin da ke jibge a yankin.
A yankin karamar hukumar Dange-Shuni kuwa, Maharan sun kai hari garin Wababe, suka harbe wani mai tabin hankali, sannan suka fasa shaguna tare da satar kayayyaki da dabbobi.
Akan hanyar su ta wucewa kauyen Rumbus ma, sun kashe Nura Ali Dogo, akan hanyarsa ta komawa gida tare da wani mutum guda, sannan suka tisa keyar wasu Karin mutune biyu.
Mazauna yankunan sun bayyana cewa harin na Dange Shuni ya kawo firgici a kauyuka irin su Sokondu, Majiyya Gida, da Bellar Koli, bisa wannan dalili mutane da dama sun kaurace wa gidajensu.
Duk da haka, jama’ar kauyukan sun yi kira ga gwamnati da ta samar da jami’an tsaro na dindindin a yankunan su domin ba su damar komawa gonakinsu da gudanar da al’amuran yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
Kawo wannan lokaci, rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto ta bayyana cewa tana cigaba da bincike a kan lamarin, ta bakin kakakin ta, DSP Ahmad Rufai.