Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, FCT, ta ce ta kama wata mata da ake zargi da zuba wa makwabciyarta ruwan zafi, lamarin da ya jawo mata mummunan rauni da ƙonewa a baya.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Satumba 2026 a Lugbe, Abuja, bayan wata takaddama tsakanin wadda ake zargi da makwabciyarta, kan amfani da wani ɓangare na filin gidan da suke zaune tare.

A cewar ’yan sanda, wadda ake zargin ta ɗauke tukunyar ruwan zafin da ke kan murhu zuwa ɓangaren da aka ware mata, abin da ya fusata.

Binciken farko na ’yan sandan ya nuna cewa wadda ake zargin ta ɗauki tukunyar ruwan zafin daga kan murhun, sannan ta zuba ruwan a bayan makwabciyarta, lamarin da ya yi mata mummunar ƙonewa.

Rundunar ta ce yanzu haka wadda lamarin ya shafa na samun kulawar likitoci saboda raunukan da ta samu.

’Yan sandan sun ce an gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu, inda aka bayar da umarnin tsare ta a cibiyar gyaran hali ta Suleja, yayin da aka ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga Satumba 2026.

Kwamishinan ’yan sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya yi kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya tare da yin haƙuri wajen warware sabani.

Ya kuma gargadi mazauna Abuja da su guji ɗaukar doka a hannunsu ko amfani da tashin hankali wajen magance rikice-rikice, yana mai cewa ya kamata a bi hanyoyin da doka ta tanada.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallansu, tare da gaggauta kai rahoton mutanen da ake zargi ko ayyukan da ba su dace ba zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *