Mahukuntan Tanzania sun ce sun kama ‘yan Burundi 134 a yankin Mara da Geita, a wani samame da aka gudanar domin gano baƙin haure da ake zargin suna zaune a ƙasar ba tare da bin ƙa’idojin shige da fice ba.
Ofishin kula da shige da fice na yankin Mara ya tabbatar da kamen ga kafar yada labaran Tanzania ta Daily News.
Jami’an sun ce sun gudanar da samamen ne a sassa daban-daban na yankin domin gano mutanen dake zaune ko gudanar da ayyuka a ƙasar ba bisa ka’ida ba.
Mataimakiyar Kwamishinar Shige da Fice, Bernadetha Tyetyetye, wadda ke jagorantar aikin, ta buƙaci jami’ai su kasance masu ƙwarewa da bin doka yayin da suke ƙara tsaurara matakan dakile shige da fice ba bisa ka’ida ba.
Ta ce matakan na da muhimmanci wajen kare tsaron ƙasa da al’umma.
Hukumomin Mara sun ce za a ci gaba da sintiri da samame a sassa daban-daban, tare da kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda suke zargin yana zaune a Tanzania ba bisa ka’ida ba.
Matakin Tanzania ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Kenya ta fara wani samame kan wasu ‘yan kasashen waje da ke gudanar da ƙananan sana’o’i.
-
Wacce rawa Ƙasar Jordan ke takawa a rikicin Gabas ta Tsakiya
-
FRSC ta ƙaddamar da yunƙurin kawo ƙarshen lodin wuce kima
-
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutum biyu bisa zargin kisa
A Kenya, Shugaba William Ruto ya umarci ‘yan kasashen waje da ke aikin tallace-tallace a titi, ƙananan shaguna da sauran sana’o’in da ba sa bukatar babban jari da su dakatar da ayyukan.
Ma’aikatar Kasuwanci ta Kenya ta kuma yi gargadin cewa samun damar shiga ƙasar ba tare da biza ba ba yana nufin mutum yana da izinin yin aiki ba.
Matakin Kenya ya haifar da fargaba tsakanin wasu ‘yan kasashen waje da ke kasuwanci a ƙasar.
An kuma yada hotuna da bidiyo da ke nuna wasu ‘yan Burundi da Rwanda da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo suna barin wuraren kasuwancinsu.
Gwamnatin Burundi ta nuna rashin amincewa da yadda ake kula da ‘yan ƙasarta, tana neman Kenya ta tabbatar da kariyarsu.
Ministan Harkokin Wajen Burundi, Edouard Bizimana, ya yi gargadin cewa idan abin da ya kira kalaman ƙiyayya kan Burundi suka ci gaba, hakan na iya shafar yadda ake kula da ‘yan Kenya dake Burundi.
Kungiyar East Africa Law Society kuwa ta yi kira da a tabbatar da cewa matakan doka sun fi karkata kan karya dokar shige da fice, ba wai a yi wa mutum hukunci saboda ƙasarsa ba.
Matakan da Kenya da Tanzania ke ɗauka sun sake haifar da muhawara kan yadda za a daidaita bin dokokin shige da fice da kuma kare haƙƙin ‘yan ƙasashen Gabashin Afirka na yin zirga-zirga da neman abin rayuwa a yankin.